03/09/2026
💔 Abin da ya faru da Pablo García a Spain abin takaici ne matuƙa.
Pablo ya kasance a Real Betis tun yana da shekaru 6 kacal. Shi ne ɗan wasa ɗaya tilo a tarihin kulob ɗin da ya taɓa zura ƙwallo a dukkan matakan matasan kulob ɗin, inda ya ci fiye da ƙwallaye 400 a makarantar horas da matasan Betis.
A makon da ya gabata ma, ya ci ƙwallonsa ta farko a La Liga tare da babbar ƙungiyar Real Betis, a wasan da s**a kara da Valencia.
Amma komai ya canza a ranar rufe kasuwar musayar ’yan wasa.
Domin samun damar yin rijistar wasu ’yan wasa da kuma daidaita harkokin kuɗi, Betis ta yanke shawarar sayar da Pablo García zuwa Racing Santander.
An hasko Pablo a kyamara yana barin hedkwatar kulob ɗin cikin matuƙar damuwa da hawaye. Har ma mahaifiyarsa, wadda ke tuƙi a baya, an gan ta tana kuka.
Magoya bayan Betis sun fusata sosai. Pablo García mai shekaru 20 an tilasta masa barin kulob ɗin da yake ƙauna ba zato ba tsammani kulob ɗin da ya shafe shekaru 14 na rayuwarsa a cikinsa.
💔 Kulob ɗin da ya yi watsi da ’yan wasan da ya horar da kansa, kulob ne da ke iya rasa makomarsa...