03/06/2026
🚨🔥 SABABBIN DOKOKIN KOFIN DUNIYA NA 2026 DA FIFA TA TABBATAR! 🌍🏆
An tabbatar da wasu manyan sauye-sauye da za su fara aiki a gasar Kofin Duniya ta 2026. Ga dokokin da za su iya sauya yadda ake buga ƙwallo gaba ɗaya! 👇
⏳ JIFAR KWALLO (THROW-IN) – SAKANNI BIYAR 5 KACAL!
Idan ɗan wasa ya yi gangancin ɓata lokaci wajen jefa ƙwallo, alkalin wasa na iya bai wa abokan hamayya ƙwallon.
🥅 BUGUN GOAL-KICK – SAKANNI BIYAR 5 KACAL!
Haka nan idan an yi gangancin ɓata lokaci yayin bugun goal-kick, ana iya hukunta ƙungiyar da ba wa abokan hamayya bugun kusurwa (corner kick).
🔄 CANJIN ƊAN WASA – SAKANNI GOMA 10 KACAL!
Ɗan wasan da ake cirewa yana da daƙiƙa 10 ne kawai ya fita daga filin wasa ta mafi kusa hanya. Idan ya ƙi fita cikin lokaci:
❌ Sabon ɗan wasan ba zai shiga ba na tsawon minti daya 1.
⚠️ Kuma ƙungiyarsa za ta ci gaba da wasa da mutum 10!
🏥 JINYAR ƊAN WASA A WAJE – MINTI 1!
Duk ɗan wasan da likitan ƙungiya ya kula da shi a filin wasa dole ya kasance a waje na tsawon daƙiƙa 60 kafin ya dawo. Sai dai akwai wasu keɓancewa ga masu tsaron gida da wasu yanayi na musamman.
🤐 RUFAR BAKI YAYIN MUHĀWARA? JA KATI NA IYA BIYO!
Idan ɗan wasa ya rufe bakinsa yayin wata takaddama ko muhawara da abokin hamayya, alkalin wasa na iya hukunta shi har da jan kati!
📺 VAR ZAI IYA BINCIKEN CORNER KICK
Na'urar VAR za ta iya tabbatar da ko an bayar da corner daidai ko akasin haka kafin a ci gaba da wasa.
🟨🟥 ZA A IYA SAKE DUBA JA KATIN DA YA FITO DAGA YELLOW BIYU
Idan an kori ɗan wasa saboda yellow cards biyu, za a iya sake duba yellow na biyu domin tabbatar da hukuncin ya dace.
👀🔥 Wadanne daga cikin waɗannan sabbin dokoki ne kuke ganin za su fi kawo cece-kuce a Kofin Duniya na 2026?
Ku bayyana ra'ayinku a comments! ⬇️💬