14/08/2026
EL-KANEMI WARRIORS FC ZA TA HALARCI GASAR NFF SUPER SIX A JOS
Kungiyar El-Kanemi Warriors FC, wadda ake wa lakabi da Alfaharin Arewacin Najeriya, za ta halarci gasar NFF Super Six da za a gudanar a birnin Jos, Jihar Plateau.
Gasar, wadda Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ke shirya wa, an tsara ta ne domin bai wa kungiyoyin Najeriya da za su wakilci ƙasar a gasannin nahiyar Afirka cikakkiyar shiri kafin fara kamfen dinsu na CAF.
El-Kanemi Warriors FC ta yi wasa a gasar nahiyar Afirka karo na ƙarshe a shekarar 2024, bayan ta lashe Kofin Shugaban Tarayya (President Federation Cup) inda ta doke Abia Warriors FC. A halin yanzu, Yaran Babagana Umara Zulum na ci gaba da samun horo mai tsanani karkashin jagorancin sabon kocin da aka dauka mai lasisin CAF A Licence, King Emmanuel.
Alfaharin Arewacin Najeriya ta kuma kara karfafa tawagarta ta hanyar daukar wasu fitattun ‘yan wasa masu kwarewa da gogewa yayin da shirye-shiryen ke ci gaba.
Da yake magana bayan kammala atisayen yau, Mataimakin Kocin El-Kanemi Warriors FC, Koci Ishaq Hussain Goni, ya ce:
«“Alhamdulillah, wasu mutane sun yi shakku cewa ba za mu iya kai wa wannan matakin da wuri ba, amma da yardar Allah yanzu muna da ‘yan wasa mafi inganci kuma cikakku a shirye wadanda suke shirye su sanya rigar rawaya da kore. Mun kara tsananta atisayenmu, kuma za mu ba duniya mamaki.»
«“Ba da jimawa ba za mu gabatar da sabbin ‘yan wasanmu, kuma In Sha Allah dukkan ku za ku yi murmushi. Burinmu shi ne mu yi nisa a gasar nahiyar Afirka. Idan gasar NNL ta fara, burinmu shi ne mu samu daya daga cikin tikitin hawa zuwa Premier League.”»
Kungiyoyin da za su halarci Super Six:
1. El-Kanemi Warriors FC
2. Enugu Rangers FC
3. Rivers United FC
4. Shooting Stars FC
5. Plateau United FC
6. Mighty Jets FC
Za a buga dukkan wasannin a Sabon Filin Wasa na Jos (New Jos Stadium).
Alfaharin Arewacin Najeriya a shirye take. Mafarkin nahiyar Afirka na ci gaba.