12/07/2026
Shirin faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Maza zuwa ƙasashe 64 zai samu cikakken nazari ne bayan kammala Gasar Kofin Duniya ta 2026, inda shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya bayyana cewa ya kamata gasar ta kasance “ta duniya baki ɗaya” kuma ta ba ƙasashe da dama damar shiga.
An fara gabatar da wannan shawara ne a bara, kuma Infantino ya ce nasarar da aka samu daga sabon tsarin gasar mai ƙasashe 48 ya nuna cewa lokaci ya yi da FIFA za ta duba yiwuwar gudanar da gasar zuwa ƙasashe 64.
A cewarsa, Kofin Duniya na farko da aka buga a tsakanin ƙasashe 48 ta kasance babbar nasara, inda ya yi nuni da cewa ƙasashe tara cikin goma daga nahiyar Afirka sun kai zagayen ’yan 32.
A shekarar 2017, FIFA ta amince da ƙara yawan ƙasashen da ke halartar gasar daga 32 zuwa 48.
A watan Afrilu na 2025, Hukumar Kwallon Kafa ta Kudancin Amurka (CONMEBOL) ta gabatar da ƙudiri a hukumance na faɗaɗa gasar ta 2030 zuwa ƙasashe 64, amma har yanzu FIFA ba ta yanke hukunci kan batun ba.
Za a gudanar da Gasar Kofin Duniya ta 2030 ne galibi a Spain, Portugal da Morocco, yayin da za a buga wasannin buɗe gasar guda uku na farko a kasashen Argentina, Uruguay da Paraguay, domin bikin cika shekaru 100 da fara Gasar Kofin Duniya. Kasar Uruguay ce ta karɓi bakuncin gasar ta farko a shekarar 1930.
TANGA SPORTS 360