03/09/2026
🚨 SABON BAYANI: ’Yan wasan da za su fara buga gasar UEFA Champions League a karon farko daga wannan kakar za su sanya wata alamar “DEBUT” ta musamman a rigarsu. 👀
🔵 Za a sanya wannan alama mai launin shuɗi ne a wasan farko na ɗan wasan kawai a Champions League.
Bayan ya buga wasansa na farko, za a cire launin shuɗin, amma kalmar “DEBUT” za ta ci gaba da kasancewa a cikin ƙaramin akwati mai launin toka. 🔁🔵
🃏 A matsayin wani ɓangare na sabon shirin UEFA, bayan wasan za a ƙara wannan alamar debut a kan katin ciniki (trading card) na ɗan wasan.
☝️ Wannan matakin ya biyo bayan ra'ayin FIFA, wadda ta gabatar da irin wannan debut patch ga ’yan wasan da s**a fara buga Kofin Duniya a karon farko a bazarar da ta gabata.
— 'ar Wasanni