22/07/2026
Ɗan Shekara 60 Ya Mutu A Hotel Bayan Ya Shiga Da Matashiya Ƴar Shekaru 20
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce ta fara gudanar da bincike kan mutuwar wani mutum mai shekara 60 da ya rasu a wani otal da ke birnin Dutse a ranar Talata, 21 ga Yuli, 2026.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa marigayin ya shiga otal ɗin tare da wata mata mai shekara 20. A cewarsa, mutumin ya fara fama da matsalar numfashi bayan ya nemi abinci.
Sanarwar ta ce an garzaya da shi Babban Asibitin Dutse, inda likitoci s**a tabbatar da rasuwarsa. Rundunar ta kuma bayyana cewa an samu wasu nau'ikan abinci, abubuwan sha, kayayyakin marigayin da kuma wani sinadari da ake zargin na ƙarfin maza ne a cikin ɗakin otal ɗin.
'Yan sanda sun ce an miƙa gawar mamacin ga iyalansa domin gudanar da jana'iza, yayin da matar da ta kasance tare da shi ke ci gaba da bai wa jami'an bincike haɗin kai.
Rundunar ta buƙaci al'umma da su guji yaɗa jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar da su ba, tana mai jaddada cewa bincike kan lamarin na ci gaba.
🥹🥹🥹🥹