Wasas tsakeyar mako

Wasas tsakeyar mako Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Wasas tsakeyar mako, Football Stadium, Shanono, Kano.

Labari: Roméo Lavia zai yi jinyar akalla makwanni shida saboda raunin da ya ji a idon sawun sa a atisayen makon jiya.  A...
11/09/2023

Labari: Roméo Lavia zai yi jinyar akalla makwanni shida saboda raunin da ya ji a idon sawun sa a atisayen makon jiya. Alamu na farko bayan gwaje-gwajensa sun nuna cewa Lavia ya sami rauni na ligament. [AdrianJKajumba]

© Wasan tsakeyar mako

Antony ya Kara bada sabon bayani game da halin da yake ciki."Na yi magana da Ingrid a WhatsApp. Lokacin da ta je Portuga...
11/09/2023

Antony ya Kara bada sabon bayani game da halin da yake ciki.

"Na yi magana da Ingrid a WhatsApp. Lokacin da ta je Portugal don halartar bikin zagayowar ranar haihuwar dan uwanta, ta nemi da ta zo nan Manchester domin haduwa da ni, domin tana son haduwa da ni sosai, sannan ta tambaye ni shin ko na fi son jajayen kaya ko fari? Na sayi tikiti kuma na tanadar mata otal. Kuma tabbas na hadu da ita a otal din kuma mun yi haduwa ta kud da kud da yarda da juna."

"Bayan wannan haduwar, ta dage cewa mu sake haduwa saboda wasu abubuwan da aka tsara, ban sake ganinta ba tun daga wannan lokacin, yayin da ta koma Brazil. Tun daga nan ban sake haduwa da ita ba. Duk wadannan bayanan da na fada a yanzu babu shakka gaskiya ne, sun tabbata akwai su a cikin sakonnin WhatsApp, duk da cewa akwai abubuwa wadanda ban bayyana su ba don kare hakkin sirri. Zan samar da hanyoyin da s**a dace don tabbatar da rashin laifi na”.

©️ Wasan tsakeyar mako

Ga Barawo ga mai kaya.......  tsakeyar mako
11/09/2023

Ga Barawo ga mai kaya.......

tsakeyar mako

Tsohon kocin Mata na kasar Spain Jorge Vilda wanda aka kora ya bayyana burin sa na son horar da Real Madrid, kamar yadda...
11/09/2023

Tsohon kocin Mata na kasar Spain Jorge Vilda wanda aka kora ya bayyana burin sa na son horar da Real Madrid, kamar yadda ya fada wa Radio MARCA.

Real Madrid za ta nemi sabon koci a bazara mai zuwa, inda kwantiragin Carlo Ancelotti zai kare a karshen kakar wasa ta bana.


© Wasan tsakeyar mako

Vini yace inaaaa, ba za'a barshi a baya ba.. ya kuka ga wannan wankan?©️ wasan tsakeyar mako
11/09/2023

Vini yace inaaaa, ba za'a barshi a baya ba.. ya kuka ga wannan wankan?

©️ wasan tsakeyar mako

Romeo Lavia yana fatan buga wasansa na farko a Chelsea bayan hutun kasashen duniya. Dan wasan tsakiyar Belgium ya samu r...
11/09/2023

Romeo Lavia yana fatan buga wasansa na farko a Chelsea bayan hutun kasashen duniya.

Dan wasan tsakiyar Belgium ya samu rauni a idon sawunsa.

Ana sa ran Lavia zai kasance a cikin 'yan wasan da za su kara da Bournemouth a karshen mako mai zuwa, amma duk da haka har yanzu akwai shakku sosai.

© wasan tsakeyar mako

Mai tsaron ragar Real Madrid Thibaut Courtois na cigaba murmurewa cikin nasara, kamar yadda ya wallafa a shafin sa na In...
11/09/2023

Mai tsaron ragar Real Madrid Thibaut Courtois na cigaba murmurewa cikin nasara, kamar yadda ya wallafa a shafin sa na Instagram.

©️ wasan tsakeyar mako

Lamine Yamal: "Nico Williams ya bukace ni da in gode masa saboda taimakon da yayi min na zura kwallo. Ina fatan wannan n...
11/09/2023

Lamine Yamal: "Nico Williams ya bukace ni da in gode masa saboda taimakon da yayi min na zura kwallo. Ina fatan wannan ne farko kuma ina fatan in lashe kofuna da dama da wasanni da dama, na zura kwallaye da taimakawa ga tawagar kwallon kafar kasar gwargwadon iko."

© wasan tsakeyar mako

Address

Shanono
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Wasas tsakeyar mako posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share