07/05/2026
Assalamualaikum Global Football Academy Players,
Muna farin cikin sanar daku cewa ranar Monday zamu dawo training kamar yadda muka saba, Insha Allah.
Mun fuskanci wani ƙalubale a baya, amma Alhamdulillah an samu gyara kuma komai yana tafiya yadda ya kamata yanzu. Wannan lokaci ne na sake haɗuwa domin cigaba da aiki tukuru, ƙoƙari da kuma gina makomar mu a football.
Ina kira ga dukkan players su kasance cikin shiri, su kiyaye lokaci, su zo da ƙwazo da discipline domin cigaban academy ɗin mu mai albarka.
Allah ya bamu nasara, ya karemu daga dukkan matsaloli, ya sanya albarka a cikin wannan academy. Ameen.