Barca Hausa

Barca Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Barca Hausa, Sports Team, Kano.
(3)

Shafin magoya bayan Barcelona 🔵🔴
🤗| Sannunku da zuwa
🌎| Shafin Barca na farko a ƙasar Hausa
💙| Ƙungiyar da babu kamarta a duniya
📰| Don sahihan labarai
🏟️| Gidan ƴan amana

🚨✅️An cire Xavi daga tawagar tsoffin taurarin Barcelona (Barça Legends) saboda matsayinsa na baya-bayan nan kan zaɓen sh...
11/06/2026

🚨✅️An cire Xavi daga tawagar tsoffin taurarin Barcelona (Barça Legends) saboda matsayinsa na baya-bayan nan kan zaɓen shugaban kulob.

Tsohon kocin Barcelona an hana shi bayyana a wasannin Barça Legends biyu na ƙarshe da aka buga a Miami da Seoul, kuma alamu na nuna cewa wannan hanin zai ci gaba a wasanni masu zuwa ma.

Mutumin da ke kula da jerin sunayen ‘yan wasan shi ne Alejandro Echevarría.

Xavi ya nemi ya shiga wasannin biyu, amma kulob ɗin ya ƙi kuma ya sanar da shi cewa “ba a maraba da shi.

Xavi bai ji daɗin lamarin ba, yayin da kulob ɗin ke cewa wannan matsala ce ta ɗan lokaci kuma za a warware ta da lokaci. 🔵🔴(Javi Miguel)

Me zakuce anyiwa Xavi adalci Kuwa?

FT: 🏴󠁧󠁢󠁥󠁮󠁧󠁿 England 3-0 Costa Rica 🇨🇷Anthony Gordon: 1 Goal, 1 Assist. 🚨🎯
10/06/2026

FT: 🏴󠁧󠁢󠁥󠁮󠁧󠁿 England 3-0 Costa Rica 🇨🇷

Anthony Gordon: 1 Goal, 1 Assist. 🚨🎯

🚨✅| Yanzu-Yanzu: Sabon ɗan wasan Barcelona Anthony Gordon ya ci wa Ingila ƙwallo ta biyu. Izuwa yanzu ya ci ƙwallo 1 San...
10/06/2026

🚨✅| Yanzu-Yanzu: Sabon ɗan wasan Barcelona Anthony Gordon ya ci wa Ingila ƙwallo ta biyu. Izuwa yanzu ya ci ƙwallo 1 Sannan ya taimaka anci ƙwallo 1. ⚽🔥

✍🏻 Lluis Carrasco (TV3): "Shin da gaske Yuro miliyan 150 za mu lale mu siyi ɗan wasan gaba mai tsawon santimita 170 kaca...
10/06/2026

✍🏻 Lluis Carrasco (TV3): "Shin da gaske Yuro miliyan 150 za mu lale mu siyi ɗan wasan gaba mai tsawon santimita 170 kacal? Anya kuwa muna cikin hayyacinmu?"

"Wai shin akan Maradona suke magana ne, Ko kuma Julián Álvarez ɗin nan da muka kalla yana buga La Liga a kakar nan? Ai idan a kan alƙaluman bajinta ne, Fermín ma ya fi shi ƙoƙari."

"Da zunzurutun kuɗi har Yuro miliyan 150, Ai za a iya siyan kusan duk wani FITACCEN ɗan wasa da ake ji da shi a faɗin Turai."

"Maimakon siyan Julián Álvarez akan wannan kuɗin, Gara mu sayi Olise mu saka shi a gefen dama, Mu yi amfani da Lamine a tsakiya a matsayin 'false nine', Sannan mu jefa Gordon a gefen hagu..."

"Idan aka yi haka, Tabbas Zamu kawo gagarumin sauyi a tsarin kai hare-harenmu!"

🚨 A HUKUMANCE: Ƙungiyar Barça ta sanar da aniyarta ta neman karɓar baƙuncin wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Turai (UEFA Ch...
10/06/2026

🚨 A HUKUMANCE: Ƙungiyar Barça ta sanar da aniyarta ta neman karɓar baƙuncin wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League) na shekarar 2029.


~~~~ TALLA:

"A yanzu babu wani App me sauƙin Data da katin waya kamar wannan, Ga Sauƙi ga inganci kuma Babu Charges.

𝗠𝗧𝗡 Alburhandatasub
𝟭𝗚𝗕 ₦250 𝗩𝗮𝗹𝗶𝗱𝗶𝘁𝘆: 1 day
1GB ₦400 𝗩𝗮𝗹𝗶𝗱𝗶𝘁𝘆: 7 d𝗮𝘆𝘀
2GB ₦800 Validity 7 days
3GB ₦𝟭,200 Validity 7 days
𝟱GB ₦1700 Validity 30 days

𝗙𝗮𝘀𝘁 • 𝗔𝗳𝗳𝗼𝗿𝗱𝗮𝗯𝗹𝗲 • 𝗥𝗲𝗹𝗶𝗮𝗯𝗹e

Kanada wayar Android? To yi maza ka Downloading ɗinsa ⤵️

Application 🖇️ link
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.Alburhandatasub_tm&pcampaignid=web_share

Our Whatsapps Contact Customer Care at
09168161535

Mun shirya tsaf don fuskantar gasar Kofin Duniya na 2026! ✅🇪🇦
10/06/2026

Mun shirya tsaf don fuskantar gasar Kofin Duniya na 2026! ✅🇪🇦

👀.Kuyi duba izuwa ga Bellingham 😳😳
10/06/2026

👀.Kuyi duba izuwa ga Bellingham 😳😳

Lamine Yamal 🇪🇸😄
10/06/2026

Lamine Yamal 🇪🇸😄

✍🏻 Javi Miguel (Diario AS): Araújo, Kyaftin marar alkibla!"Bai dace ba kwata-kwata ace ɗan wasa yayi tafiyar kilomita 20...
10/06/2026

✍🏻 Javi Miguel (Diario AS): Araújo, Kyaftin marar alkibla!

"Bai dace ba kwata-kwata ace ɗan wasa yayi tafiyar kilomita 20,000 (zuwa da dawowa) don kawai a duba lafiyar shi na ƴan awanni, Ana saura kwanaki biyar kacal a fara World Cup. Amma idan ana zancen Ronald Araújo ne, komai zai iya faruwa. Wannan wani zaɓi ne mai ban mamaki kuma marar kan gado."

"Wannan ba shi ne karo na farko da Araújo ya tsinci kansa a irin wannan yanayin ba. Bayan mummunan wasan da ya buga a Gasar Zakarun Turai (Champions League) da Chelsea inda aka ba shi jan kati, Rahotanni sun ce ya kwashe watanni biyu yana jiyyar matsalolin damuwa (mental health) domin ya dawo daidai."

"Yanzu haka ɗan wasan ba ya cikin tsare-tsaren koci Flick, Kuma bai dace da salon wasan Bielsa ba."

"Da za a sami wanda zai gaya masa gaskiya, Da ya nuna masa cewa akwai rayuwa bayan Barça, Kuma zai iya dawo da takunsa idan ya koma wani gurin. Misali, a gasar Serie A ta Italiya, inda ƙungiyoyi s**a fi yin tsaron gida a baya kusa da ragarsu; hakan zai sa ba zai riƙa barin sarari a bayansa da abokan hamayya za su riƙa gudu ba."

"Mutum na farko da ya fara tona masa asiri shi ne Luis Enrique a cikin shirin fim ɗinsa (documentary), lokacin da ya ce: 'Ku ƙyale shi kawai, domin shi ne ɗan wasa mafi rauni wajen sarrafa ƙwallo a Barça.' Kuma hakan ta tabbata a filin wasa daga baya, lokacin da ya yi kuskuren ba da fas aka ƙwace ƙwallon, sannan aka koro shi da jan kati sa'ilin da yake ƙoƙarin gyara kuskurensa."

"Ko ma dai yaya abin yake, ya kamata kyaftin ya riƙa auna shawararsa da kyau. Domin wannan ɗanyen hukunci da ya ɗauka ya ɓata sunan likitocin motsa jiki na tawagar ƙasar Uruguay. Haka take faruwa idan ka kasance kyaftin marar alkibla!"

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Barca Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category