25/11/2021
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Mbappe da Bale da Werner da Lacazette da Lingard, Traore da Ziyech.
Dan wasan gaba na Paris St-Germain da Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, zai iya barin ƙungiyar idan kwantirginsa ya kare a lokacin bazara, inda Newcastle United ta shiga jerin masu sha'awarsa. (Express).
Dan wasan gaba na gefe na Chelsea Hakim Ziyech, dan Moroko mai shekara 28, da kuma dan gaban Jamus Timo Werner, mai shekara 25, sun kasance wadanda Barcelona za ta nema a madadin Raheem Sterling, na Manchester City, idan kungiyar ba ta samu nasarar janye dan Ingilar mai shekara 26 ba a watan Janairu. (ESPN).
Paris St-Germain ta yi watsi da bukatar farko da Manchester United ta gabatar kan kociyanta Mauricio Pochettino
(Manchester Evening News).
Tsohon kociyan Tottenham, Pochettino, mai shekara 49, sai ya jira akalla wata shida kafin ya k**a aiki da United. (Star).
Manchester United din ta tattauna da tsohon kociyan Borussia Dortmund Lucien Favre da tsohon mai horas da Lyon Rudi Garcia kan aikin wucin-gadi. (Telegraph).
Wadanda kungiyar ta Old Trafford take zawarci da aikin na rikon kwarya har da tsohon kociyan RB Leipzig Ralf Rangnick da tsohon kociyan Roma Paulo Fonseca. (Mail).
A cire wani zane na hoton kociyan United da aka kora Ole Gunnar Solskjaer daga Old Trafford. (Sun).
Liverpool da Barcelona na sha'awar dan gaban Chelsea Christian Pulisic, mai shekara 23, amma kuma Blues ba za ta sayar da shi ga wata kungiya abokiyar hamayyarta ba a Premier, kuma ita Barcelona ba ta da yuro miliyan 50 da za ta sayi dan wasan gaban na gefe dan Amurka. (El Nacional).
Chelsea ta tattauna da dan bayan Fenerbahce da Hungary Attila Szalai, mai shekara 23. (Football Insider).
Wolves za ta saurari masu bukatar sayen dan gabanta na gefe dan Sifaniya Adama Traore, mai shekara 25, a watan Janairu. (Football Insider).
Aley Abs