Salah El Deen

Salah El Deen ๐˜๐€๐‘๐„๐„๐Œ๐€๐Ž47

ZINA TA YI ARHA, AURE YA YI TSADA.Yau idan kana da N500,000 a aljihunka, da wuya wannan kuษ—in su ishe ka ka yi aure sabo...
06/05/2026

ZINA TA YI ARHA, AURE YA YI TSADA.

Yau idan kana da N500,000 a aljihunka, da wuya wannan kuษ—in su ishe ka ka yi aure saboda tsadar al'ada, kayan lefe, da shirye-shiryen biki da muka kakaba wa kanmu. Amma abin takaici da tashin hankali; da N50,000, N10,000, ko ma kalaman daษ—in baki kawai, zaka iya kai yarinyar mutane ษ—akin hotel domin ka biya buฦ™atar haram. Subhanallah...

Mun wayi gari a cikin wata al'umma da muka tsananta abin da Allah Ya sauฦ™aฦ™a (Aure), sannan muka sauฦ™aฦ™a abin da Allah Ya haramta (Zina).

Wannan gaskiya ce mai ษ—aci wacce dole ne mu fuskance ta ta fuska uku:

1. Zuwa Ga Iyaye:
Don Allah a duba tsarin da ake ษ—ora wa matasa masu neman aure. Yawan buฦ™atun maฦ™udan kuษ—aษ—e da gasar biki sune suke tsoratar da samari masu kishi da natsuwa. Wannan matsin lissafin shine yake sa yara mata su daษ—e a gida har shaiษ—an ya samu damar jefa su a halaka. Sauฦ™aฦ™a aure shine babbar garkuwar al'umma daga rushewa.

2. Zuwa Ga 'Yan Mata:
'Yar uwa, ki san darajar kanki, Jikinki da mutuncinki sun fi ฦ™arfin N50k, shawarma, ko sayen sabuwar wayar hannu. Kada ki yarda wani ษ“ataccen namiji ya sayi lahirarki da ษ—an abin duniya da zai ฦ™are a rana ษ—aya. Duk namijin da ba zai iya zuwa wajen iyayenki ya neme ki da aure ba, baya ฦ™aunarki, yaudararki kawai zai yi ya watsar.

3. Zuwa Ga Samari:
Dan'uwa, ka ji tsoron Allah, Kuษ—in da kake ษ“atarwa wajen kai matan mutane hotel, idan ka tara su wallahi zasu iya yi maka aure na halas ka samu natsuwa a rayuwarka. Ka tuna cewa duk abin da ka yi wa 'yar wani, akwai wanda shima yake jiran 'yarka ko ฦ™anwarka a gaba.

Dole ne mu farka daga wannan baccin, mu koma kan tsarin addininmu kafin musiba ta gama mamaye mu gaba ษ—aya.

Allah Ya sauฦ™aฦ™a mana al'amuran aure, Ya raba mu da kowace irin hanyar alfasha.

4โƒฃ7โƒฃ

DARUSAN DA KUKA JIMA KUNA JIRA.. Da farko ina son ka nutsu, ka ajiye duk wani abu da kake yi a gefe, ka bani cikakken ha...
21/04/2026

DARUSAN DA KUKA JIMA KUNA JIRA.. Da farko ina son ka nutsu, ka ajiye duk wani abu da kake yi a gefe, ka bani cikakken hankalinka. Darusa ne masu tsananin ษ—aci, amma idan ka hadiye su kayi aiki dasu, ko an wayi gari kowa ya guje ka, zaka yi rayuwa cikin 'yanci

Na farko, Ka gane cewa babu wanda yake son ka saboda KAI, kowa yana son ka ne saboda abin da zaka iya yi masa ko irin farin cikin da kake sa shi a ciki. Ranar da karfinka ya kare baka da abin bayarwa, a ranar zaka gane cewa babu tsantsar soyayya a duniya sai ta mahaifiya.
Na biyu, Duk irin alakar da ke tsakaninka da mutum, kada ka yarda ka dora lissafin arzikinka ko nasararka a kansa. Iyayenka, 'yan uwanka, ko abokan arziki, duk zasu iya canzawa ko su mutu su bar ka a yanke. Tashi ka gina kanka da karfinka, ta yadda koda kowa ya guje ka, zaka iya tsayawa da kafafunka babu fargaba.
Na uku, Mutumin da yake kokarin ganin bayanka ba daga sama zai fado ba. Karkai mamakin wanda kuke dariya daya, kuke cin abinci guda, wanda ya san irin ribar da kake samu, shine zai fara jin haushin ci gabanka a boye saboda baya son ka wuce shi.
Na hudu, Namijin da ya auri mace domin kyawun fuskarta kawai ba tare da duba hankalinta da natsuwarta ba, tamkar mutumin da ya sayi gida ne saboda kyawun fenti ba tare da duba karfin harsashin ginin ba. Idan fentin ya kankare, asarar ta bayyana.
Na biyar, ka fahimci cewa Asalin halin mace yana bayyana ne a lokacin da namijin da take tare dashi ya dawo bashi da ko sisi. Shi kuma namiji Asalin halinsa yana bayyana ne a lokacin da ya samu komai na rayuwa a hannunsa(kuษ—i/muฦ™ami), dan haka wanan canjin ba sabon hali bane, zamani ne kawai ya goge masa makeup.

A ฦ™arshe, zaka iya kyamatar wannan gaskiyar kaci gaba da gina rayuwarka a kan kuskure, amma ina tabbatar maka; wata rana duniya zata tilasta maka koyon wadannan darussan a aikace, kuma a lokacin zakai kuka da nadama. Wannan ba rubutu ne na neman a burge ka ba, allurar farkarwa ce na coka maka ita.
4โƒฃ7โƒฃ

21/04/2026
21/04/2026

Wata Macen sai tayi sati babu Data, Maza kuduba mai sunan mahaifiyarku albarkacin wannan Sunan, A sa mata Data 1GB๐Ÿฅฐ

โ€œWelcome to Kano โ€“ Heart of Northern Nigeria โค๏ธโ€4โƒฃ7โƒฃ
21/04/2026

โ€œWelcome to Kano โ€“ Heart of Northern Nigeria โค๏ธโ€
4โƒฃ7โƒฃ

๐‘จ๐’๐’๐’‚๐’‰ ๐’š๐’‚ ๐’‹๐’Š๐’Œ๐’‚๐’๐’Œ๐’‚ ๐’Œ๐’‚๐’Ž๐’‚๐’ ๐’‚๐’ƒ๐’๐’Œ๐’Š ๐’‚๐’๐’๐’‚๐’‰ ๐’š๐’‚๐’”๐’‚ ๐’„๐’†๐’ ๐’š๐’‚๐’‡๐’Š๐’Ž๐’‚๐’Œ๐’‚ ๐’๐’‚๐’....4โƒฃ7โƒฃ
21/04/2026

๐‘จ๐’๐’๐’‚๐’‰ ๐’š๐’‚ ๐’‹๐’Š๐’Œ๐’‚๐’๐’Œ๐’‚ ๐’Œ๐’‚๐’Ž๐’‚๐’ ๐’‚๐’ƒ๐’๐’Œ๐’Š ๐’‚๐’๐’๐’‚๐’‰ ๐’š๐’‚๐’”๐’‚ ๐’„๐’†๐’ ๐’š๐’‚๐’‡๐’Š๐’Ž๐’‚๐’Œ๐’‚ ๐’๐’‚๐’....
4โƒฃ7โƒฃ

KA KULA DA ZUCIYAR KA DOMIN BA KOWACE IRIN MACE BACE TA DACE DA GURBI A CIKIN TAMatashi ka sani zuciyar ka ba filin wasa...
21/04/2026

KA KULA DA ZUCIYAR KA DOMIN BA KOWACE IRIN MACE BACE TA DACE DA GURBI A CIKIN TA

Matashi ka sani zuciyar ka ba filin wasa ba ce, ba wuri ne da kowa zai shigo ya fita yadda ya ga dama ba.

A yau, mutane da yawa suna baiwa soyayya muhimmanci amma sun manta da tsaron zuciyarsu.

โ€ข Ba kowace mace da ta nuna kulawa take nufin ta dace da kai ba.
โ€ข Ba kowace dariya take nufin gaskiya ba.
โ€ข Ba kowace kusanci yake nufin makoma ba.

Wasu suna shigowa ne don su ษ—auki lokaci, ko su ษ—auki kulawa, ko su bar maka rauni aciki.

Gaskiya mai ษ—aci:
zuciya mai sauฦ™in buษ—ewa tana da sauฦ™in karyewa.

Shi yasa dole ka koyi lura da halaye ba kalamai kaษ—ai ba, ka bada lokaci kafin ka yarda da kowa, ka daina baiwa kowa gurbi a zuciyarka cikin sauri.

Domin wani lokacin, abin da kake kira soyayya gwaji ne kawai.

Zuciyarka na da daraja ka bada ita ga wanda ya cancanta, ba wanda ya zo kawai ba don cika manufa ba.

Tambaya:
Shi wai a ganinku, me ya fi sa mutum saurin bada zuciyarsa a soyayya?

4โƒฃ7โƒฃ

๐”ฝโ„๐•€๐”ป๐”ธ๐• ๐•„๐•†๐•„๐”ผโ„•๐•‹
02/01/2026

๐”ฝโ„๐•€๐”ป๐”ธ๐• ๐•„๐•†๐•„๐”ผโ„•๐•‹

โ—ขโ—โ—ข โ—ขโ–”โ—ฃ โ—ขโ–”โ—ฃโ—ขโ–”โ—ฃ โ—ขโ–”โ—ฃ โ—ขโ–”โ—ฃโ–ˆโ—ฃโ–ˆ โ–ˆโ–โ–ˆ โ—ฅโ—ฃโ—โ–ˆโ–โ–ˆ โ–ˆโ–โ—ค โ–ˆโ–โ–ˆโ–ˆโ—ฅโ–ˆ โ–ˆโ–”โ–ˆ โ—โ—ฅโ—ฃโ–ˆโ–”โ–ˆ โ–ˆโ–”โ—ฃ โ–ˆโ–”โ–ˆโ—ฅโ—โ—ฅ โ—ฅโ—โ—ฅ โ—ฅโ–โ—คโ—ฅโ—โ—ฅ โ—ฅโ—โ—ฅ โ—ฅโ—โ—ฅ๐Ÿ™๐™”๐™– ๐˜ผ๐™ก๐™ก๐™–๐™ ๐˜ผ ๐˜ฟ๐™ช๐™  ๐™จ๐™–๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ข๐™ช๐™ ๐™– ๐™ง๐™–๐™จ๐™–โœ...
05/03/2023

โ—ขโ—โ—ข โ—ขโ–”โ—ฃ โ—ขโ–”โ—ฃโ—ขโ–”โ—ฃ โ—ขโ–”โ—ฃ โ—ขโ–”โ—ฃ
โ–ˆโ—ฃโ–ˆ โ–ˆโ–โ–ˆ โ—ฅโ—ฃโ—โ–ˆโ–โ–ˆ โ–ˆโ–โ—ค โ–ˆโ–โ–ˆ
โ–ˆโ—ฅโ–ˆ โ–ˆโ–”โ–ˆ โ—โ—ฅโ—ฃโ–ˆโ–”โ–ˆ โ–ˆโ–”โ—ฃ โ–ˆโ–”โ–ˆ
โ—ฅโ—โ—ฅ โ—ฅโ—โ—ฅ โ—ฅโ–โ—คโ—ฅโ—โ—ฅ โ—ฅโ—โ—ฅ โ—ฅโ—โ—ฅ

๐Ÿ™๐™”๐™– ๐˜ผ๐™ก๐™ก๐™–๐™ ๐˜ผ ๐˜ฟ๐™ช๐™  ๐™จ๐™–๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ข๐™ช๐™ ๐™– ๐™ง๐™–๐™จ๐™–
โœ๏ธ๐˜ผ๐™—๐™ž๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ข๐™ช๐™ ๐™š๐™จ๐™ค ๐™ ๐™ค๐™ ๐™ข๐™ช๐™ ๐™š ๐™—๐™ช๐™ง๐™ž๐Ÿคฆโ€โ™‚๏ธ
๐Ÿคฒ๐™†๐™–๐™จ๐™–, ๐™ข๐™ช๐™ฉ๐™ช๐™ฃ๐™– ๐™™๐™–๐™˜๐™š๐™ฌ๐™– ๐™ง๐™–๐™๐™–๐™ข๐™–๐™ง๐™ ๐™–โšก
๐Ÿ™Œ๐™๐™–๐™›๐™ž ๐™†๐™–๐™ง๐™›๐™ž๐™ฃ ๐˜ฟ๐™ช๐™  ๐˜ผ๐™—๐™ž๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ข๐™ช๐™ ๐™– ๐™ง๐™–๐™จ๐™–โš 
๐Ÿ™๐™”๐™– ๐˜ผ๐™ก๐™ก๐™–๐™ ๐™†๐™–๐™Ÿ๐™–๐™ง๐™–๐™— ๐™˜๐™š๐™ข๐™ช ๐™™๐™–๐™ž- ๐™™๐™–๐™žโœ๏ธ
๐Ÿ”‘๐™„๐™ข๐™–๐™ฃ๐™ž๐™ฃ, ๐™ข๐™ช ๐™จ๐™–๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™ ๐™–๐™จ๐™– ๐™ข๐™ช๐™›๐™ž ๐™ ๐™–๐™ง๐™›๐™ž๐™ฃโš’
โค๏ธ๐™•๐™ช๐™˜๐™ž๐™ฎ๐™–๐™ฃ ๐™ข๐™ช ๐™ ๐™–๐™จ๐™– ๐™ข๐™ช๐™œ๐™–ma ๐™™๐™–๐ŸŒŽ๐™ก๐™›๐™ฎ

๐‘จ๐’๐’๐’‚๐’‰ ๐’š๐’‚ ๐’‹๐’Š๐’Œ๐’‚๐’๐’Œ๐’‚ ๐’Œ๐’‚๐’Ž๐’‚๐’ ๐’‚๐’ƒ๐’๐’Œ๐’Š ๐’‚๐’๐’๐’‚๐’‰ ๐’š๐’‚๐’”๐’‚ ๐’„๐’†๐’ ๐’š๐’‚๐’‡๐’Š๐’Ž๐’‚๐’Œ๐’‚ ๐’๐’‚๐’....
17/01/2023

๐‘จ๐’๐’๐’‚๐’‰ ๐’š๐’‚ ๐’‹๐’Š๐’Œ๐’‚๐’๐’Œ๐’‚ ๐’Œ๐’‚๐’Ž๐’‚๐’ ๐’‚๐’ƒ๐’๐’Œ๐’Š ๐’‚๐’๐’๐’‚๐’‰ ๐’š๐’‚๐’”๐’‚ ๐’„๐’†๐’ ๐’š๐’‚๐’‡๐’Š๐’Ž๐’‚๐’Œ๐’‚ ๐’๐’‚๐’....

May Allah protects us from any of an evils acts and shaytan
01/12/2022

May Allah protects us from any of an evils acts and shaytan

Address

Dryport
Kano
BLISSFUL

Telephone

+2349124181428

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Salah El Deen posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Salah El Deen:

Share