19/05/2025
MUHIMMAN ABUBUWA GUDA 10 DANGANE DA NICO PAZ DA BA KOWA NE YA SANI BA.
1. An Haife Shi a Sifaniya, Amma Yana Wasa da Ƙungiyar Ƙasa ta Argentina. Duk da cewa an haifi Nico Paz a Tenerife, Sifaniya, ya zaɓi wakiltar Argentina a matakin ƙasa, don girmama asalin mahaifinsa.
2. Mahaifinsa, Pablo Paz tsohon ɗan Wasan ƙwallon ƙafa ne, inda ya wakilci Argentina a Gasar Cin Kofin Duniya ta 1998, kuma ya buga kwallo a ƙungiyoyi da dama a Sifaniya, ciki har da CD Tenerife.
3. Ya Shiga Real Madrid Yana da Shekaru 16. Ya koma Real Madrid La Fábrica (makarantarsu ta matasa) daga Tenerife a 2016, inda ya yi fice da sauri saboda ƙwarewarsa.
4. Ya Ci Kwallo a Wasan Farko na Champions League. A watan Nuwamba 2023, Nico ya fara buga gasar Champions League tare da Real Madrid kuma ya ci kwallo mai ban mamaki.
5. Ana Kwatanta Shi da Kaká da Fede Valverde. Saboda saurinsa, iya kai hare-hare, da kyakkyawan salon wasa, ana kwatanta shi da tsohon tauraron Brazil Kaká, yayin da wasu ke ganin yana da irin ƙoƙarin Fede Valverde.
6. Nico Paz na iya amfani da ƙafa biyu hagu da dama a wasan kwallo, yana iya bugawa, tsalle, da wucewa da kowacce ƙafa ba tare da matsala ba.
7. Hukumar kwallon ƙafa ta Sifaniya ta nemi ya wakilce su, amma ya ƙi kuma ya nuna biyayyarsa ga Argentina.
8. Duk da kasancewarsa ɗan wasan tsakiya mai kai hare-hare (No. 10), Nico Paz na iya taka rawa a matsayin ɗan tsakiya ko kuma a gefe, gwargwadon tsarin da ake so.
9. A lokacin da yake atisaye tare da manyan 'yan wasa na Real Madrid, ya samu horo daga shahararrun 'yan wasa kamar Modrić da Kroos wanda hakan ya taimaka masa sosai.
10. A yanzu haka Real Madrid na shirin koma da shi daga Como akan kuɗi €8 miliyan, saidai iyalinsa sun bayyana cewa suna so ya zauna shekara ɗaya a can domin ya cigaba da bunƙasa cikin kwanciyar hankali ba tare da wani ƙalubale ba.
Shin me zaku ce akan wannan labari?
19/05/2025
Sen. Karaye