23/05/2026
Idan kana karanta Al-Qur'ani a hankali kana lura da messages and messagers wato sakon Ubangiji da kuma wadanda Allah ya baiwa sakon su isar. Zaka ga cewa Ubangiji yana da tsarin bayar da Annabta ko Manzanci ga 'dan garin da ake so suyi Imani, ko kuma 'dan Kabilar, misali;
1. Game da Adawa (mutanen Annabi Hudu), sai Allah yace "Zuwa ga Adawa mun aika musu 'dan uwan su Hudu".
2. Samudawa (mutanen Annabi Salihu), sai yace "zuwa ga Samudawa mun aika da dan uwan su Salisu".
3. Mutanen birnin Madayana (mutanen Annabi Shu'aibu), sai Allah yace "zuwa ga birnin Madayana mun aika da dan uwan su Shu'aibu".
Abinda nake in nuna mana shine, Allah yayi ta cewa 'dan uwan su, wato kaso 98 na Annabawan da Allah ya aika ya aike su ne zuwa ga mutanen garin su, Kabilar su, Yaren su, 'dan uwan su.
A cikin Suratu Ibrahim Allah yace "babu wani Manzon da muka aike shi face da Yare (language) din mutanen sa ya tafi, domin yayi musu bayanin sakon".
Wato "Bi Lisani kaumihi"
بلسان قومه
Da harshen mutanen sa.
Daga cikin hikimar yin haka itace;
Idan ana so Da'awah ta karbu, mutane su fahimci sakon da aka kawo musu toh ayi musu da Yaren da suke ji, a aika musu da wanda zai iya yin magana fluently da Yaren su, saboda shi ya san mutanen sa, suma sun sanshi, da zaran yayi bayani zasu gane zasu fahimta cikin sauki.
Idan ka dauki Bahaushe kace yaje yayi wa'azi da yaren Igbo ba za'a samu abinda ake so ba sai dai in dama a cikin ya tashi, yana yin Yaren kamar yadda suke yi, kuma ya fahimce su. In ba haka ba babu yadda za'a yi su gane b***e su karba.
Haka kuma idan kace kai mutumin birni zaka je kauye ka koyar dasu, na farko harshen ka ba zai zama dai dai da nasu ba, watakil akwai abubuwan da dole kayi amfani da kalmar Turanci, sannan shigar ka da Tufafi ka dole zata bambanta dasu, hakan zai kara girman barrier of understanding tsakanin ka dasu.
Toh haka muke fama a bangaren Da'awah a yau, mutane da yawa zasu shiga Musulunci amma koyar dasu shine babban aiki. Duk wanda ya shigo Musulunci kuma aka koyar dashi Musulunci a cikin watanni shida (six months) toh in sha Allah zai tabbata kuma ya dauwama a cikin Musulunci.
Amma sabanin haka toh da wahala su iya zama a cikin Musuluncin, koda sun zauna zasu zama cikin wadanda basu san komai game da addinin su ba.
Sai dai, yaya za'a yi a koyar dasu?
Dole ayi koyi da salo ko strategy da Allah yayi bayani a Al-Qur'ani, shine aje a dauko wasu daga cikin mutanen kauye da s**a Musulunta a shigo dasu cikin gari, cikin birni, ayi camping dinsu na watanni 6 a koyar dasu, idan sun goge sai su koma kauyukan su don su koyar da Musulunci da Yaren su.
Sai dai yin hakan yana bukatan a Gina babbar Islamic center, ayi wajen da za'a Gina dakunan kwana, Azuzuwa, Masallaci, Abincin su, abun shan su, Syllabus, daukan nauyin Malaman da zasu karantar dasu na watanni shidan. Wannan kuma zai ja miliyoyin kudade masu yawan gaske.
Idan ba'a samu haka ba dole a cigaba da local system na daukan mutanen birni suna zuwa kauyuka suna koyarwa suna dawowa gari.
Wannan tsarin shima da nasa kalubalen, shine wasu wuraren suna da nisa da birni ko bakin babban T**i, kafin ka shiga dajin kaje ka koyar har ka fito Awanni ne masu yawa, abu na biyu ana bukatan Ababen hawa, Motorcycle ko Babur masu yawa, mota Hilliux da 'kananan Motoci.
Kaga duk wata ko duk sati sai anyi fueling an saka Man Fetur. Sannan idan kuka je kauyen most of the time sai kun je kun hado kan mutanen, saboda wasu sun tafi Gona, wasu kasuwa, wasu suna wajen wani wasa, mutanen kauyuka kadan ne zasu tara mutanen su idan sun san zaku zo koyar dasu ilimi.
Idan kuma kace zaka tura Malamai suje su zauna a kauyen suyi wata daya ko biyu suna koyarwa dole ka dauki nauyin iyalan su da s**a bari a gida, dole ka kula da security din Malaman daka tura din, domin ba zaka tura su kauye haka kawai ba tare da security plans da tsari mai kyau ba.
Dole ka dauki nauyin Abincin su, da Magani idan rashin lafiya ta taso.
Aiyuka ne masu yawan gaske, masu wahala, idan bamu yi ba toh makiyan mu zasu yi, kuma kauyukan dake gefe da manyan biranen mu zasu shiga wasu addinan daban daban. Domin mutanen su ba zama s**a yi ba, suna aiki kamar yadda wasu Musulmi suke yi domin yin kira zuwa ga addinin su a nan Arewa da muke rayuwa.
Mutane su shigo Musulunci ba abu ne mai wahala ba, amma a koyar dasu har su tabbata a Musulunci da ilimi shine abu mai wahala, kuma mai cin kudi da lokaci sosai. Wadannan dai aiyuka ne da muke fatan Allah ya bamu ikon yin abinda zamu iya kafin ajali yazo mana, domin ba zasu kare ba.
Aiyuka ne da a rana daya zasu ci kudi mai yawa idan aikin za'a yi sosai yadda ya kamata, b***e a sati, wata ko shekara. Wadannan wasu ne daga cikin kalubalen mu a fagen Da'awah da kuma bukatun mu, muna addu'a Allah ya bude mana Kofar arziki da zamu yi haka domin daukaka addinin mu da kuma neman kada a wajen Allah.
Allah yasa mu dace.
Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo Prof. Adam Muhammad Abubakar Adamu Musa Kore Shaikh Abubakar Gummi School Asadulhifz Ruky Precious