13/02/2024
Wasu Kurakuren Da Maza Magidanta Suke Tafkawa Kuma Ko Ajikinsu:
SHARE 🔔
Bama dabi'a ba, sun ma maidasu tamkar abune na wajibi su aikata hakan.
Wadannan dabi'un suna da matukar wahala a samu wani namijin da bai da wasu daga cikinsu. Dabi'un nan sune kamar haka:
1: Kula mata da sunan da sunan namiji mijin mata hudu ne. Wannan bai zama dalilin da Kaine can kaine nan ba. Amma kana da mace ko mata ba aure kake da niyar yi ba amma ana ganinka da wasu matan. Wannan kuskure ne.
2: Ka kashe kudi a waje amma a gidanka matsolo kake.
Idan kana tare da abokanka ko 'yan matanka baka shakkar kashe kudi, amma kanada shiga gida ka dawo babu.
Kaje kana ciyar da wasu da basu da hakki a kanka abubuwa masu dadi. Amma gidan ka suna cin abinci ko nama babu. Wannan kuskure ne.
3: Murtuke fuska shima yana cikin genden kuskuren da wasu maza magidanta suke yi.
Idan suna waje dariya da shewa babu kaukautawa, da sun shigo gida sai su hada fuska ko kada mace ta raina su. Wannan bayaga kuskure ne babba, har ila yau jahilci ne da gabanci ga duk namiji mai irin wannan halin.
4: Wasu mazan ba zaka taba ganinsu sun fita sun jera da matansu, ko sun shiga mota tare ba domin yin wani ziyara, dubiya ko shakatawa. Gani suke agansu da matansu tare faduwan ajine. Amma yana barin gidansa zai iya zuwa wajen wata da zai sa a gaban mota su tafi shan 🍨. Kuskure ne babba.
5: Akwai wani kuskuren da wasu mazan ke yi na kin wadata matansu da iyalansu da suturan sawa daga Sallah sai Sallah.
Babu wani abun burgewa da zaka hana matarka tayi maka kwalliya mai kyau, amma zaka kalli wasu matan na waje da s**a yi shiga mai kyau kana sha'awar su.
Wadata iyalinka da sutura da kayan kwalliya ba asaran kudi bane, domin haka Allah (SWT) Ya umurta maza suyiwa matansu. Shiyasa ma Ya haramta wasu mazan su kalli kwalliyar da matarka zata maka.
Idan kana cikin irin mazan nan 'yan gargajiya daga Sallah sai Sallah to ka daina saboda kuskure ne.
6: Rashin yin wasu shawarwari da matarka nan