23/08/2026
Iran ta ce zata kai kari kan kamfanonin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya muddin ta sanya mata takunkumi
Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Mohsen Rezaei, ya fitar da wata sanarwar gargaɗi da ke bayyana cewa duk ƙasar da ta shiga cikin shirin takunkumin tattalin arzikin da Amurka ke shirin ƙaƙaba wa ƙasarsa, za ta fuskanci mataki mai tsanani.
Wannan jawabi na Rezaei ya zo ne biyo bayan sauyin shugabanci a Majalisar Tsaron, inda aka naɗa shi sabon sakatare da nufin tunkarar sabbin ƙalubalen da ke gaban ƙasar.
Wannan taƙaddama ta samo asali ne bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar ƙaddamar wani sabon yaƙi ta fannin takunkumin tattalin arziki mafi tsanani a tarihi kan Iran.
Amurka na ƙoƙarin tursasawa abokan hulɗarta da sauran ƙasashn da ke alaƙar kasuwancin man fetur da Iran, musamman kasar China wadda ke sayen kashi mafi tsoka na man ƙasar, da su dakatar da duk wata hulɗar kasuwanci da ita.
A cikin jawabinsa, Rezaei ya jaddada cewa idan ƙasashe maƙwabta s**a goyi bayan Amurka, Iran za ta toshe Mashigar Hormuz da yankin Tekun Fasha baki ɗaya, ta yadda ba za a bar ko ɗigon ɗanyen ya fita zuwa ƙasashen duniya ba.
Ya bayyana cewa Iran za ta ɗauki duk ƙasar da ta taimaki Amurka a matsayin abokiyar gaba da za a shigar da ita cikin jerin ƙasashen da za a kai wa hari.
Haka itama gwamnatin Iran ta tsara matakai guda uku na mayar da martani, inda za ta fara da lallashi da tattaunawa da ƙasashen domin su janye jikinsu daga shirin Amurka. Idan har kasashen s**a ki amincewa da hakan, Iran ta yi barazanar ƙaddamar da hare-haren soji kai tsaye kan muhimman ayyukan tattalin arzikinsu domin durkusar da su.