Dutsinma Coaches Association DUCA

Dutsinma Coaches Association DUCA Welcome To The Official Page Dutsin-ma United football club Slowly but surely

26/03/2022

TPL USMAN NADADA: Gaskiya Matakin Nasara

Daga Alƙalamin Jikamshi

Har yau, har gobe, daga cikin ire-iren abubuwan da na karanta a karan-kai na daga Kwamishinan Filaye da Safiyo na jihar Katsina, Alhaji Usman Nadada, shi ne kokarin kwatanta adalci a yayin da ya ke mu'amala da Jama'a.

Kamar misali, zan iya tunawa a dalilin aiki na, Alhaji Usman Nadada ya yi man wani abu, da a wajen mutum biyu ne kadai Mafi akasari za ka same shi: walau dai Mahaifan ka ko kuma mutumin da ya yi riko da adalci ya Kuma kaucewa son zuciya.

Abinda ya faru kuwa shi ne wata magana da ya taba gaya man a ofishin sa lokacin ya na rike da matsayin Janar Manaja na Hukumar Tsara Birane da Yankuna: "Hajji Garba ka ga dai bakin gwargwado Allah ya yi ma ka basira da nasibi a wannan aikin na ku na Jarida.

Bakin gwargwado mutane sun san ka kuma su na respecting abinda ka ke, to shawarar da zan ba ka a nan ita ce kar ka sake ka tsugunnar da kan ka a tsarin aikin jarida na aikin gwamnati kawai, a maimakon hakan ka yi amfani da damar da ka ke da ita wajen cin moriyar baiwar da Allah Ya yi ma ka, ta hanyar kafa wata cibiya ta wannan aikin na ku mai zaman kan ta.

Ka ga kenan idan ka tashi aiki, ka na da wajen da za ka je ba wai yawo haka nan a gari ba ko zaman majalisa.

Sannan Kuma Hakan zai ba ka damar samun Yan kudaden shiga outside albashin ka. Kar ka sake a yaudare ka da wasu yan kudi da Wani zai ba ka, kashe ma ka zuciya kawai za su Yi, idan ka na da Wani private outfit har al'umma ma sai ta fi karuwa da Kai".

Ya Yi man wannan maganar daga ni sai shi a office, sannan ya maimaita man ita a wasu lokutan a tattare da sauran Yan Jarida abokan aiki na.

Irin wannan maganganun ba kasafai a kan ji su daga bakin Yan siyasa ko manyan ma'aikatan gwamnati ba.

Abinda a ka saba gani shi ne, idan an ga ka na da wata baiwa da wani Dan siyasa zai karu da ita, to fa zai san yadda zai kalallame ka ne, ya dankwarar da kai waje guda, ya Yi ta tatsar wannan baiwar ta ka don cigaban kan shi, shi kadai.

Daga ranar da ya gama cin moriyar ganga, to fa zai jefar da kwauren ta. Sanin kowane, wannan wata halayya ce da a ke kuka da ita musamman a tsakanin Yan siyasa.

Irin wannan exceptional quality, daya tamkar da goma, da na gani da Ido na daga Usman Nadada, ita ce ta sanya har yau, har gobe ni ke ganin kimar shi da mutuncin shi, domin na san ba ni kadai ya taba yi ma ita ba, ya yi ma wasu ma a gaba na.

Don kara tabbatar man da cewa, da gaske ya ke a shawarar da ya ba ni, a lokacin da na yi joining Ziima Communication a matsayin jami'in tuntuba, har Ziima din Alhaji Usman Nadada ya je, ya yi program, ya Kuma Yi ma na fatan alheri da cigaba a business din mu.

Ko shakka babu, mu na da bukatar mutane ma su irin wannan kyakyawar zuciyar a cikin wannan al'ummar ta mu.

A nawa lissafin, ba lallai ba ne sai da babban mukami Alhaji Usman Nadada zai taimaki al'umma ko gina matasa ba, ya na yin Hakan tun kafin ya shiga siyasa tsundum.

Shi ya sa idan na tashi addua, ni kan ce, abinda ya ke shi ne mafi alheri ga Alhaji Usman Nadada da al'ummar jihar Katsina, Ubangiji Ta'ala Ya tabbatar da shi, don kuwa mu kan so abu sai ya zamo ba shi ne mafi alheri ba, sannan mu ki abu a karshe ya zamo shi ne mafi alherin.

Ya Allah Kai ne mafi sanin alkhairi, Allah ga Alhaji Usman Nadada.

24/03/2022

Ƙoƙarin Hon. Usman Nadada Akan Samarda Sabon Birni Da Ma'aikatar Ƙasa Da Sufiyo Ta Jihar Katsina Zata yi

Daga Alƙalamin Yakubu Lawal

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya bai yi shinge ko iyaka akan cewar sai wanda ya kware a Ma'aikata ko sashe ake nadawa ba mukami a matsayin Mamba na majalisar zartaswa a matakin jiha ko Tarayya.

Sai dai idan aka yi gamo-da-katar abin ya fi haifar da mai ido idan aka baiwa mutuminda ya fi kwarewa a Ma'aikata ko sashe da aka nada shi ya Jagoranta.

Ma'aikatar Kasa da Sufiyo ta Jahar Katsina, na daga cikin wuraren da s**a dace da kwararren Jami'in Tsara Birane(Town Planner) da ke shugabantar Ma'aikatar, wato TPL. Usman Nadada.

Wannan dama da Tpl.Usman Nadada ya samu bayan shekarun da ya dauka yana aiki mai alaka da tsara birane tun bayan kammala karatunsa na digiri na daya da na biyu, wanda har ya kai shi ga rike kujerar Janar Manajan Hukumar Tsara Birane da yankuna na jihar har Katsina na tsawon shekaru ya sanya yake da ra'ayi na ganin cigaban harkokin da s**a jibanci Kasa da Sufiyo.

Kudurori da Manufofin da TPL Usman Nadada ya hau mukamin kwamishinan Ma'aikatar da su na tunanin dorawa daga inda wanda ya gada ya tsaya a kan inganta tsarin Kasa sune sirrin nasarorin da ya ke cigaba da samu a Shugabantar Ma'aikatar.

Wannan tsari kuwa shi ne, sarrafa Kasa kai tsaye a maimakon rarrabawa ba tare da sarrafawa ba.

A karkashin wannan tsari ne aka yi tunanin samarda wani sabon birni da zai kunshi kayan more rayuwa dabam-daban da mutanen da za a haifa a sabuwar duniyar za su amfana da su.

Wannan sabon birni da za a kafa a Arewacin garin Katsina, a kan hanyar Katsina zuwa Jibia an rada masa suna'KATSINA RACE COURSE VILLAGE'

Idan wannan birni ya kammalu zai kunshi Gidaje, Makarantu,Massallatai gami da Filayen Wasanni dabam-daban, musamman na Wasannin tseren Dawaki da na Kwallon Dawaki.

Shedar yiwuwar wannan aiki tuni Ma'aikatar Kasa ta yi yarjejeniya da wani kamfanin tuntuba na wasu kwararrun masu ilmin tsara birane mai suna 'BIN-HAJJ CONSULT' da ya samarda taswira ta zahiri da bayyana kwarangal din birnin baki daya.

Tuni wannan taswira ta samu sambarka da amincewar Maigirma Gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari da Maimarbata Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da sauran masu ruwa da tsaki.

Wani abun da ya kamata mutane su sani shi ne tuni an fara rattabawa takardun yarjejeniyoyi hannu da kamfanonin da ke huldar samar da muhalli(Developers) don cigaba da tabbatuwar samuwar wannan sabon birni.

Irin wannan shirye-shirye wadanda duniyar cigaba s**a yi nisa ga aiwatar da su,a kasashe irin namu na ifrikiyya ba a cika samun aiwatar da su dari bisa dari ba.

Don haka, kaifin basira da hikima ta Kwamishinan Kasa da Sufiyo a Jahar Katsina Tpl.Usman Nadada ya yi amfani da kwarewar da ya ke da ita ta wannan fuska ya hannanta kula da tafiyar ga Kamfanin BIN-HAJJ CONSULT don haka ta cimma ruwa.

Wani sabon salo da Tpl. Usman Nadada ya yi wa wannan aiki tare da shawarar abokan aikinsa da kuma amincewar gwamnati shi ne wannan birni shi zai samarda kansa da kansa.

Yanzu nan da wasu 'yan lokutta da yardar mai duka sabon birni zai wanzu a nan Katsina,sai dai sanin karkashin wace gunduma zai kasance, muna jiran masana tsare-tsaren iyakoki su bayyanas.

Ko ba komai, ajiye kwarya a bisa gurbinta ta kara tabbata a Ma'aikatar Kasa da Sufiyo ta Jahar Katsina

Alkalamin: Yakubu Lawal
Dan Jarida
Jami'in Hulda da Jama'a.

28/12/2021

Innahlillahi wa'innah ilaihin raji'un Amadadin wannan kungiya Mai suna kamar haka Dutsin-ma Coaches Association (DUCA) Tare da Chairman Alhaji Dayyab Labo (Sigini) da sauran Exco da Coaches da Official na Harkar Wasanni na Karamar Hukumar Dutsin-ma Muna Mika sakon Ta'aziyar mu ga dukkan daukachin Ahalin Gidan Alhaji Aminu Balbalo bisa ga rasuwar shi Ubangiji Allah ya jikan shi yayi mashi rahama yasa Chan ta fiye mashi nan

Innahlillahi wa'innah ilaihin raji'uhn Amadadin wannan kungiya Tun daga Exco Official da Members na daukachin Clubs din ...
31/03/2021

Innahlillahi wa'innah ilaihin raji'uhn Amadadin wannan kungiya Tun daga Exco Official da Members na daukachin Clubs din Karamar Hukumar Dutsin-ma Muna Mika sakon gaisuwa ga yan'uwan Malam Sani Abdullahi Tsauri (Landy) Wanda Allah ya amshi rayuwar shi Muna Addu'ar Allah ya jikan shi yayi Mai rahama yasa Chan ta fiye mashi Nan Dan alfarmar annabi Mohammed saw)

Arc Ahamed Musa Dan'giwa Associate Unity Inter Zone Cup Competition Dutsin-ma Zone 2020 Quarter Finel.  Today March Duts...
23/11/2020

Arc Ahamed Musa Dan'giwa Associate Unity Inter Zone Cup Competition Dutsin-ma Zone 2020 Quarter Finel. Today March Dutsin-ma United 'A' Vs Darby Stars Kurfi At Lawal Wowo Town Ship Stadium Time 4:00pm Gate Fees #50 Come one Come All

07/11/2020
21/09/2020

Do you need something as stunning as this ?

DM us let's talk Business 💸

Address

Dutsin-Ma

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dutsinma Coaches Association DUCA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dutsinma Coaches Association DUCA:

Share