14/05/2026
LABARI DA DUMI DUMI:~ Rikici ya kunno kai tsakanin shugaban La liga Javier Tebas da shugaban Real Madrid Florentino Perez.
Javier Tebas yace akwai takaici mutum kamar Florentino, ya je kafafen watsa labarai yana zabga ƙarya cewa hukumar La liga bata son Real Madrid, wannan babbar ƙaryace inji shi.
Shugaban na La liga ya ƙara da cewa kowa yasan shi riƙaƙƙen masoyin Real Madrid ne dan haka yana taya Madrid alhinin rashin samun nasarar cin kofin La liga.