05/08/2026
Aurelien Tchoumeni ya saki sanarwa a hukumance bayan abun da ya faru tsakanin sa da Valverde:
“Abun da ya faru wannan makon a filin ɗaukar horo, ba abu bane da za a amince da shi ba.
Na faɗi hakanne yayin da nake tunani a kan misalin da za mu barwa matasa masu tasowa, ko dai a ƙwallon ƙafa ko kuma a makaranta. Koma waye akan daidai koma waye bashi da gaskiya, kamata yayi a ko da yaushe mu kalli menene masalaha domin kawo ƙarshen tashin hankali.
A gaba da komai, ina ba da haƙuri kan baƙin fentin da muka shafawa ƙungiyar nan. Na san cewa magoya baya, ma'aikata, abokan wasa na, manajojin, da kowa da kowa sun ji ɓacin ran yadda kakar wasan nan ta kasance. Amma ɓacin rai ba zai sa mu ji huciyar raɗaɗin da muke ji ba. Irin wannan abun, ko da zai faru a ɗakin sanya tufafin kowacce ƙungiya, bai kamata ya faru a ɗakin sanya tufafin Real Madrid ba. Musamman tun da Real Madrid ita ce ƙungiyar da aka fi magana akan ta a duniya.
Kafofin sadarwa na jin daɗin wallafa labaran ƙarya, don haka kada ku yarda da komai da aka faɗa domin ƙarya tafi yawa.
Koma dai menene, yanzu ba lokaci ba ne da zamu tsaya magana akan waye yayi wannan, waye yace wannan, ko kuma waye mai gaskiya ko waye mara gaskiya. Na fahimce cewa an hukunta mu kuma na karɓi hukuncin da aka mana. Zamu ci gaba da zama a matsayin dangi ɗaya, tare da rashin amincewa da juna a wasu lokutan, amma dole ne mu sanya aikin ƙungiyar mu a gaba da farko fiye da kowanne irin abu daban. Na bayar da haƙuri ga tawagar ƙungiyar, sannan kuma zan ƙara miƙa neman gafarata ga dukkan masoya Real Madrid.
Yanzu lokaci ne da zamu kalli gaba, mu kuma mayar da hankali akan wasan El Clasico da kuma kakar dake gaban mu, domin dawo da ƙungiyar mu babban matsayi, inda ta saba kasancewa.”
Follow 💥💥💥⚽