Sahihan Labaran Wasanne cikin harcen Hausa

Sahihan Labaran Wasanne cikin harcen Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sahihan Labaran Wasanne cikin harcen Hausa, Track Stadium, Adamawa, Yola.

Kalaman Ruben Amorim ga magoya bayan Manchester United a filin wasa na Old Trafford bayan tashi wasansu da Aston Villa."...
26/05/2025

Kalaman Ruben Amorim ga magoya bayan Manchester United a filin wasa na Old Trafford bayan tashi wasansu da Aston Villa.

"Ina son neman afuwar ku game da yadda wannan kakar ta kasance. Na yi matukar jin ba daɗi ni da tawaga ta.
Sannan abu na biyu, ina son gode muku.
Muna matuƙar godiya da irin goyon bayan da kuka bamu a gaba ɗaya wannan kakar. Na san wasanni da yawa sun zo mana da tsauri.

"Yanzu muna da isasshen lokacin da zamu yi gyara.
Mu manta da abun da ya faru a baya, saboda kakar wasan ta ƙare, ta ƙare.
Ka da mu zargi juna, mu cigaba da tafiya tare tsintsiya maɗaurinki ɗaya mu kalli gaba.

"Watanni shida da s**a wuce, na ce zamu shiga mawuyacin hali. Yau, bayan wannan mummunar kakar wasan, ina son faɗa muku cewa kwanaki masu kyau suna nan zuwa.

"Idan akwai wata ƙungiya a duniya da a baya ta nuna zata iya shawo kan kowanne irin yanayi mai kyau ko mara kyau, to ƙungiyar mu ce. Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United.

"Na gode muku sosai - sai mun gan ku kakar wasa mai zuwa."

• Sahihan Labaran Wasanne ✍️

Address

Adamawa
Yola

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sahihan Labaran Wasanne cikin harcen Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category