15/05/2026
Tsohon Dan wasan real Madrid Casemiro ya bayyana cewa abin da ya fi bambanta ‘yan wasan Real Madrid da sauran kungiyoyi shi ne ƙarfin zuciya da jajircewa wajen tinkarar matsin lamba.
Dan wasan na Brazil ya ce a Madrid, bai isa ka kasance ƙwararren ɗan wasa kawai ba, dole ne ka kasance mai ƙarfi a tunani domin a kullum ana sa ran ka lashe manyan kofuna.
Ya bayyana cewa ko bayan lashe gasar zakarun Turai ko La Liga, nan take mutane za su fara tambayarka me kuke ganin za ku gyara don ci gaba da lashe kofuna a gaba.
Casemiro ya ce wannan matsin lamba ne ya sa ‘yan wasan Madrid ke da wani irin ƙwazo na musamman, domin kulob ɗin baya yarda da sakamako mara kyau ko gazawa na dogon lokaci.
Ya kara da cewa tarihi da girman kulob ɗin suna tilasta wa kowane ɗan wasa ya bayar da iyakar kokarinsa a ko da yaushe.
Tsohon dan wasan tsakiya na Madrid din ya kuma nuna cewa shugabanni da tsofaffin taurarin kungiyar irin su Luka Modrić, Toni Kroos da Karim Benzema sun taimaka wajen gina ruhin nasara a kungiyar, wanda har yanzu ake kokarin ci gaba da raya shi.