Hausa Update

Hausa Update "Gaskiya, Hanzari, da Amintaccen Rahoto"

“Ba ni na fara jefa ’yan Najeriya cikin wahala ba” - TinubuA jawabinsa na cika shekara 66 da samun yancin kai, Tinubu ya...
01/10/2026

“Ba ni na fara jefa ’yan Najeriya cikin wahala ba” - Tinubu

A jawabinsa na cika shekara 66 da samun yancin kai, Tinubu ya ce ya san wasu na fama da talauci har ma abincin ci yana gagararsu amma matsalar ba ta fara da gwamnatina ba “Ba ni na fara jefa ’yan Najeriya cikin wahala ba” Wahalar da ’yan Najeriya ke ciki ta samo asali ne daga shekaru da dama kuma ba za mu iya kawar da matsalar da ta taru shekaru da dama cikin shekaru huɗu ba”

Al'ummar jihar Zamfara sun fito akan tituna suna murna tare da mika godiya ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu akan nada ...
02/09/2026

Al'ummar jihar Zamfara sun fito akan tituna suna murna tare da mika godiya ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu akan nada Sanata Abdul-aziz Yari shugaban yakin neman zabensa.

Mazauna ƙaramar hukumar Borgu a Neja na tserewa zuwa jamhuriyar Benin saboda matsalar tsaroMazauna ƙaramar hukumar Borgu...
02/09/2026

Mazauna ƙaramar hukumar Borgu a Neja na tserewa zuwa jamhuriyar Benin saboda matsalar tsaro

Mazauna ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja na fara barin gidajensu zuwa Jamhuriyar Benin, sakamakon ci gaba da kai hare-hare da wasu ’yan bindiga ke yi a yankin.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa ɗan takarar jam’iyyar ADC na Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Borgu/Agwara, Murtala Haliru Dantoro, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.

Dantoro ya ce matsalar tsaro a yankin na ƙara ta’azzara, inda ake halaka mutane, satar mutane, raba jama’a da muhallansu da kuma takaita zirga-zirga da ayyukan noma s**a addabi al’ummomin yankin.

Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin “Hire From Nigeria”, da nufin samar da ayyukan yi miliyan ɗaya masu alaƙa da kas...
02/09/2026

Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin “Hire From Nigeria”, da nufin samar da ayyukan yi miliyan ɗaya masu alaƙa da kasuwannin ƙasashen waje nan da shekarar 2030.

Shirin zai haɗa ƙwararrun ’yan Najeriya, ma’aikatan fasaha, masu aikin dijital da masu fasaha da kamfanoni da ma’aikata na ƙasashen waje, domin su riƙa samun ayyukan yi daga Najeriya ba tare da sun ƙaura zuwa ƙasashen waje ba.

Gwamnati ta ce za ta mayar da hankali wajen horar da matasa, ba su takardun shaidar ƙwarewa da kuma shirya su domin gogayya a kasuwar aikin duniya.

Daraktan Kuɗi da Harkokin Mulki a Hukumar Raya Kogunan Hadejia-Jama’are, Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso, ya gwangwaje Babba...
02/09/2026

Daraktan Kuɗi da Harkokin Mulki a Hukumar Raya Kogunan Hadejia-Jama’are, Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso, ya gwangwaje Babban Hadiminsa, Musa Sale Ɗan Zaria, da kyautar sabuwar mota, kuɗi da sabbin kayan sawa.

DA DUMI-DUMI: ‘Yan Sanda Da Kwamitin Zaman Lafiya Sun Fara Sa Ido Kan Zafin Siyasar 2027Farida Abdullahi Zarma Ayau News...
02/09/2026

DA DUMI-DUMI: ‘Yan Sanda Da Kwamitin Zaman Lafiya Sun Fara Sa Ido Kan Zafin Siyasar 2027

Farida Abdullahi Zarma Ayau News

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa sun ƙara sa ido kan kalaman siyasa da za su iya haddasa tashin hankali yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa.

’Yan sanda sun fara bincike kan kalaman kwamishinan Matasa da Wasanni na Borno, Sainna Buba, shugaban Kuje, Samuel Shekwolo, da Sanata Francis Fadahunsi.

Hakan na zuwa bayan Shekwolo ya ce masu adawa da APC su bar Kuje. Daga baya, wasu ’yan daba sun kai hari kan taron Accord Party a Kuje, inda s**a lalata kayayyaki tare da jikkata mutum ɗaya.

ME ZAKU CE?

Wannan dai shi ne saƙon Kashim Shettima ga 'yan Najeriya kan bikin zagayowar ranar haihuwarsaMataimakin shugaban Najeriy...
02/09/2026

Wannan dai shi ne saƙon Kashim Shettima ga 'yan Najeriya kan bikin zagayowar ranar haihuwarsa

Mataimakin shugaban Najeriyar, ya bukaci 'yan ƙasar da ka da su siya masa kyautuka a bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Shettima, wanda ya cika shekaru 60 a ranar Laraba, ya ce masu niyyar yi masa kyauta su yi amfani da kuɗin wajen yin sadaka da kuma kyautata wa mabukata.

Me za ku ce?

Jam’iyyun adawa a Najeriya sun fara tsara yadda za su kayar da gwamnatin APC mai mulkin ƙasar ta wajen haɗakar da za ta ...
02/09/2026

Jam’iyyun adawa a Najeriya sun fara tsara yadda za su kayar da gwamnatin APC mai mulkin ƙasar ta wajen haɗakar da za ta fitar da ɗan takara ɗaya mai ƙarfi da zai iya gwabzawa da shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Address

Kano
Kunya

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Update posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share