17/11/2025
Gamayyar kungiyoyin matasa wanda ya hada da kiristoci da musulmi a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno, Gwoza Youth Forum (GYF) ta yi watsi da rahoton kisan gillar da aka yi wa kiristoci a yankin a matsayin karya da yaudara.
Taron ya bayyana cewa, yayin da rikicin Boko Haram cikin shekaru 15 da s**a gabata ya haifar da mace-mace da barna a Gwoza, hare-haren ba su da alaka da wani addini.
Bayanin hakan ya fito ne a matsayin martani ga wata sanarwa da kungiyar Kiristocin Gwoza (GCCA) ta buga mai suna “ “The Unspoken Genocide: GCCA Account on Christian Persecution in Gwoza Local Government Area, Borno State”.
Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Lahadi a Maiduguri, Shugaban GYF na kasa, Bulama Ali Haruna ya bayyana cewa al’ummomi da dama da s**a hada da Agapalawa, Amuda, Jubrili, Zamga, Angurva, Pulka, Bokko, Aiga, Dughufaka, Chikide, Barawa, Paigi, Kirawa, Ashagashiya, da Ngoshe Sama’a—anyi hare-hare kan Musulmai da Kirista.