22/06/2024
WA'AZI/NASIHA. Assalamu alaikum wa rahmatullah wa baraka tuhu. Jama'a musulmai; jin tsoron Allah (S.W.T) da inganta imani tare da tuba da bin dokokin Allah (S.W.T) wajibi ne akan kowane baligi mai hankali. Don haka idan muna son zaman lafiya a kasar mu to sai mun hada kawunan mu akan yin imani da duk wadanda shari'ar addinin musulunci ta yi umurni da a yi imani da su. Haka kuma dole ne hadin kan mu ya kasance akan shari'ar addinin musulunci, kada mu yarda mu raba kawunan mu, don Allah mu kauda gaba da kiyayya ga junan mu. Wallahi shaidan yana bakin ciki yaga mun hada kawunan mu akan addinin musulunci, kamar yanda a yanzu yake farin ciki da rarrabuwar da mu ka yi. Samun zaman lafiyar mu da cin nasara ya ta'allaka ne akan hadin kan mu.