20/08/2026
1. Manchester City da Manchester United na zawarcin Manu Koné
Manchester City ta shiga takarar neman ɗan wasan AS Roma, Manu Koné, inda ta fara zawarcinsa.
Sai dai ana ci gaba da alakanta ɗan wasan da komawa Manchester United, kamar yadda jaridar Daily Mail ta wallafa.
2. Manchester United na gab da ɗaukar Carlos Baleba
Manchester United na gab da kammala ɗaukar ɗan wasan Brighton, Carlos Baleba, kan kuɗi da ake hasashen ya kai fam miliyan 75.
Kamar yadda aka bayyana a jiya, Manchester United ta sake komawa zawarcin ɗan wasan cikin gaggawa.
Rahotanni sun ce Baleba ya riga ya amince da komawa Manchester United, bayan da aka cimma yarjejeniya ta baka da baka tsakanin ɓangarorin.
Ana sa ran ɗan wasan zai sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyar da Manchester United.
3. Berbatov ya yaba da sayayyar Manchester United
Tsohon ɗan wasan Manchester United, Dimitar Berbatov, ya bayyana gamsuwarsa da yadda Manchester United ta gudanar da kasuwar sayayya a bana.
Berbatov ya yaba da ƙoƙarin ƙungiyar wajen ƙarfafa tawagarta, inda ya ambaci ƴan wasan da s**a haɗa da Andrey Santos, Youri Tielemans da Carlos Baleba.
A cewarsa, ƙungiyar ta samu waɗannan ƴan wasan ne kan kuɗi kusan fam miliyan 150.
4. Rio Ferdinand ya hasashen wanda zai lashe Premier League
Tsohon ɗan wasan Manchester United, Rio Ferdinand, ya bayyana ra'ayinsa kan wanda yake ganin zai lashe gasar Premier League a bana.
Ferdinand ya yi hasashen cewa Arsenal ce ke da babbar damar lashe gasar, musamman duba da yadda ƙungiyar ta gudanar da kasuwar sayayya.
Ya kuma yi nuni da cewa Arsenal ta ci gaba da ƙarfafa tawagarta, inda har a jiya ta ɗauki ɗan wasa Konsa.
Ferdinand na ganin cewa Manchester United, Manchester City, Liverpool da Chelsea ba za su iya yin gogayya da Arsenal wajen neman kambun Premier League ba.
5. Paul Pogba ya bar AS Monaco
Tsohon ɗan wasan Manchester United, Paul Pogba, ya bar ƙungiyar AS Monaco bayan da aka soke kwantiraginsa.
Hakan ya biyo bayan yawan raunin da ɗan wasan ke fama da shi, wanda ya hana shi samun damar taka leda akai-akai.
Tun bayan komawarsa AS Monaco, Pogba ya buga wasanni shida kacal.
Wannan ne ya sa wasu ke kira ga ɗan wasan da ya yi ritaya daga buga ƙwallo, yayin da wasu ke ganin cewa ya kamata ya aje takalmansa saboda yana ci gaba da fama da rauni.
Sai dai matarsa, Zulay Pogba, ta mayar da martani ga masu wannan magana, inda ta ce waɗanda ke kiran Pogba da ya aje takalmansa za su ji kunya.
Game da masu cewa Pogba yana buga ƙwallo ne kawai saboda kuɗi, ta ce: “Mungode Allah, domin Allah Ya ba mu.”