02/09/2026
SPONSORED
TAWAGAR GAWUNA TA FAYYACE BATUN FICEWAR WASU ‘YAN SIYASA ZUWA APC.
Tawagar Kamfen ɗin Gawuna ta ce rahotannin da ke cewa wasu manyan magoya bayan Dakta NASIRU YUSUF GAWUNA sun fice daga JAM’IYYAR NDC domin komawa APC ba su bayyana cikakkiyar gaskiyar abinda ya faru ba.
Tawagar ta bayyana cewa mutanen da ake kira “TAWAGAR GAWUNA” sun bar Tsarin siyasar Gawuna tun watan Yunin Daya gabata, bayan da aka samu sabani kan wasu buƙatunsu na siyasa.
Ta ce tun farko mutanen sun yi ƙoƙarin kulla wata yarjejeniya da jam’iyyar ADC ba tare da sanin ko amincewar Gawuna ba, inda daga baya s**a karkata zuwa neman komawa APC.
Sai dai tawagar ta tabbatar da cewa shirye-shiryen NDC na babban zaɓen 2027 ba su dogara da waɗannan mutane ba, kuma tsarin kamfen ɗin jam’iyyar ya riga ya kafu.
Ta kuma ce tafiyar siyasar Gawuna na ƙara samun ƙarfi, inda manyan ‘yan siyasa, shugabannin al’umma da masu tasiri daga ƙananan hukumomi 44 na Kano ke ci gaba da shiga tafiyar.
Tawagar ta yi kira ga jama’a da kafafen yaɗa labarai da su yi watsi da duk wani bayani da ke danganta waɗannan mutanen da Gawuna ko tsarin NDC.
Taron dai ya Gudana ne Karkashin Jagorancin.
Dist. Sanata Saleh Adamu Kwaru
DG/Shugaban Tawagar Gudanar da Kamfen ɗin Gawuna.