10/04/2026
Rikici Ya Barke A Barau Football Club!
Ɗan wasan gaba na ƙungiyar, Yahaya Ibrahim Suleiman, ya fito karara ya bayyana halin da ake ciki a cikin ƙungiyar bayan an dakatar da shi daga buga wasa.
A cikin wata takarda da ya aike zuwa ga Babban Uban ƙungiyar, Senator Barau I. Jibrin, Yahaya ya bayyana cewa ƙungiyar na fuskantar matsaloli masu yawa waɗanda s**a haɗa da rashin adalci da kuma nuna wariya a tsakanin ‘yan wasa.
Ya zargi babban manajan ƙungiyar, Dominic Iorfa, da nuna halin rashin mutunta ‘yan wasa, magoya baya da kuma ma’aikatan ƙungiyar.
Haka kuma ya bayyana cewa akwai son rai da rashin gaskiya wajen zaɓen ‘yan wasa, lamarin da ya kawo rarrabuwar kai a cikin team ɗin.
Yahaya ya kuma bayyana cewa shi ne mafi yawan ƙwallaye a ƙungiyar a wannan kakar, sannan shi ne ya fara zura ƙwallo a gida da waje. Duk da haka, an ajiye shi ba tare da buga wasa ba kusan wasanni 15 ba tare da wani bayani mai gamsarwa ba.
Saboda wannan hali, Yahaya ya ce ya nemi a soke kwantiraginsa da ƙungiyar saboda ya rasa ƙwarin gwiwa da sha’awar ci gaba da taka leda.
Amma maimakon a saurare shi, sai aka dakatar da shi, tare da zargin cewa yana yin rashin da’a.
A ƙarshe, Yahaya ya roƙi Sanatan da ya duba wannan lamari da idon basira tare da bincike domin tabbatar da gaskiyar abin da yake faruwa a cikin ƙungiyar, sannan ya amince da buƙatarsa ta barin ƙungiyar.
Shin ya kamata a bar shi ya tafi ko kuma a warware matsalar a cikin ƙungiyar?
📸 sports news hausa