25/04/2026
Complete Football sun rahoto, a watan Oktoba, Real Madrid ta doke Barcelona kuma ta baiwa ƙungiyar tazarar maki 5 a saman teburin La Liga, amma tun daga wannan ranar komai ya lalace musu.
• Kafin nan, sun rasa wasa ɗaya ne kacal a kowacce gasa da s**a buga, kuma suna gurbi mai kyau a gasar zakarun nahiyar Turai.
• Sai Xabi Alonso ya sauya Vinicius a El Clasico, wanda ya k**a faɗa lokacin da yake barin filin wasa.
• “Tafiya zan yi! Tafiya zan yi! Zai fi kawai idan na bar ƙungiyar nan!”
• Tun daga wannan lokaci, dangantakar sa da Xabi Alonso ta yi tsamari kuma ɗakin sanya tufafin Madrid ya rikice, abun da ya haifar da sallamar kocin wata ɗaya bayan faruwar lamarin.
• Real Madrid ta ɗauko Alvaro Arbeloa, wanda ƙungiyar dake buga gasa mai daraja ta uku ta tsige shi a gasar Copa del Rey a wasan sa na farko, daga nan Bayern Munich ta tsige shi a gasar zakarun nahiyar Turai, kuma zai iya tafiya da tazarar maki 11 tsakanin sa da Barcelona idan s**a samu nasara yau.
• Yanzu Madrid ta ƙara tsintar kanta a gurbi k**ar na bara: Babu kofi, neman sabon mai horas wa, tare da babu wani tabbacin samun ci gaba a kaka mai zuwa.