Labaran Chelsea A Hausa II

Labaran Chelsea A Hausa II Mun Bude Wannan Shafi Ne Domin Kawo Labaran Chelsea Da Harshen Hausa.

🔵✨ Maresca bayan antashi 0-0: "Nayi farin ciki sosai, na gayawa 'yan wasan hakan, Nafi farin ciki fiye da wasan Brentfor...
22/12/2024

🔵✨ Maresca bayan antashi 0-0:

"Nayi farin ciki sosai, na gayawa 'yan wasan hakan, Nafi farin ciki fiye da wasan Brentford."

"Everton wasa ne mai wahala, filin wasa mai wahala, ƙungiya mai wahala, suna ɗaya daga cikin ƙungiyoyi biyar mafi kyawun tsaro a Turai ta bangaren Clean Sheets."

🔵✨ Maresca after 0-0 draw: “I’m very happy, I told this to the players. I’m more happy than the Brentford game”.

“Everton it’s tricky game, tricky stadium, tricky team, they’re one of the five best teams defensively in Europe in terms of clean sheets”.

Everton vs. ChelseaTottenham vs. LiverpoolEverton abokanan hamayyar Liverpool ne.Tottenham abokanan hamayyar Chelsea ne....
22/12/2024

Everton vs. Chelsea
Tottenham vs. Liverpool

Everton abokanan hamayyar Liverpool ne.

Tottenham abokanan hamayyar Chelsea ne.

Kuna gani Everton zasu iyayin sakarci da daga mana kafa a wasanmu da su yau, domin su yiwa Liverpool buqulu.

Tottenham suma zasu iyayin sakarci da dagawa Liverpool kafa saboda suyi mana buqulun hawa saman teburi, ko kuma zasuyi ta ‘yar gida.

A gobe Lahadi ne Chelsea zata kara da Everton a filin wasansu.Muna yiwa Chelsea fatan Nasara.Nasarar Chelsea na nufin za...
21/12/2024

A gobe Lahadi ne Chelsea zata kara da Everton a filin wasansu.

Muna yiwa Chelsea fatan Nasara.

Nasarar Chelsea na nufin zata haye saman teburin gasar Primier a karon farko tin bayan shekaru hudu da s**a wuce, da kuma karo na farko a karkashin jagorancin Todd Boehly da tawagarsa.

💙

Marc Guiu ✌️ £6 kacal muka siyo shi daga Barcelona bayan Xavi ya fito da shi daga Academy din kungiyar🥳Yanzu shine wanda...
20/12/2024

Marc Guiu ✌️ £6 kacal muka siyo shi daga Barcelona bayan Xavi ya fito da shi daga Academy din kungiyar🥳

Yanzu shine wanda yafi kowa cin Ball a gasar Conference da kwallaye 6 a wasanni 6 a gasar.

Wannan shine hat-trick dinsa na farko a rayuwarsa tare da Chelsea.

Shekarar 18 kacal

🚨⚠️ Sanarwar daga dan wasa Mykhaylo Mudryk."Zan iya tabbatar da cewa ansanar da ni cewa samfurin gwaji dana bayar ga FA ...
17/12/2024

🚨⚠️ Sanarwar daga dan wasa Mykhaylo Mudryk.

"Zan iya tabbatar da cewa ansanar da ni cewa samfurin gwaji dana bayar ga FA ya ƙunshi wani haramtaccen abu".

"Wannan yazo da cikakkiyar girgiza saboda bantaɓa yin amfani da duk wani haramtaccen abu ba ko karya kowace irin doka, ina aiki tare da ƙungiyata [Chelsea] domin bincika yadda hakan ta faru."

"Na san cewa banyi wani laifi ba kuma ina fatan zan dawo filin wasa nan bada jimawa ba."

"Ba zan iya cewa komai a yanzu ba, saboda sirrin tsarin, amma zanyi iyaka yina nan gaba bada jimawa ba."

Chelsea Vs. BrentfordKyakkyawan zubi daga Enzo Maresca.Tosin a farkon farawa (first eleven) tare da Colwell a gefensa wa...
15/12/2024

Chelsea Vs. Brentford

Kyakkyawan zubi daga Enzo Maresca.

Tosin a farkon farawa (first eleven) tare da Colwell a gefensa wanda a ganina hakan shine mafi cancanta ga kungiyar matukar Tosin zai abinda ake so.

Marasa Lafiya (Injury): Reece James, Fofana, Lavia, Mudryk, Badaichel. sai kuma Neto dakatarwa.

Jackson da Sanchez indai s**a sami katin gargadi na Yellow Card a wannan wasan to zasu rasa fafatawarmu da Everton.

Fatan Nasara ga Chelsea

- Jadon Sancho dan wasan da ake kallonsa a Man United a matsayin tashi ta kare mai.- Cole Palmer dan zaman benci a Man C...
15/12/2024

- Jadon Sancho dan wasan da ake kallonsa a Man United a matsayin tashi ta kare mai.
- Cole Palmer dan zaman benci a Man City.
- Pedro Neto dan wasan da baya rabo da rauni a Wolves.
- Nicolas Jackson dan wasan da ba a san shi ba a gasar La Liga.

Yanzu sune ‘yan wasa mafi ƙarfin kai hare-hare a gasar Premier.🔝

Rashin nasarar Liverpool a yau da kuma idan Chelsea tayi nasarar a gobe, hakan na nufin zai zama maki daya ne kacal tsak...
14/12/2024

Rashin nasarar Liverpool a yau da kuma idan Chelsea tayi nasarar a gobe, hakan na nufin zai zama maki daya ne kacal tsakanin Liverpool ta daya da Chelsea ta biyu.

Zagaye na gaba:

- Tottenham vs. Liverpool birnin London.

- Everton vs. Chelsea a birnin Liverpool

Chelsea zata iya hawa saman teburi kafin Bouncing day🔵

Munce, Ya Ubangiji🤲

'Yan wasan Leicester City sunyi Celebration irin na Cole Palmer jiya a wasansu da Chelsea a gasar cin kofin FA na matasa...
14/12/2024

'Yan wasan Leicester City sunyi Celebration irin na Cole Palmer jiya a wasansu da Chelsea a gasar cin kofin FA na matasa.

Sun chi 2-0 amma sun sha kashi daga karshe da ci 3-2..

The Leicester players dropped the Cole Palmer celebration yesterday vs Chelsea in the FA Youth Cup.

They went 2-0 up and lost 3-2. A cold exit from the competition in the 3rd round.

Thomas Frank Coach din Brentford game da Chelsea.🗣"Sune wadanda aka ayyana akan yin nasara, Maiyuwa saboda sune Team maf...
14/12/2024

Thomas Frank Coach din Brentford game da Chelsea.

🗣"Sune wadanda aka ayyana akan yin nasara, Maiyuwa saboda sune Team mafi karfi a gasar Primier a halin yanzu, ta iya kasancewa shirinsu yafi na Liverpool, dukda da cewa Liverpool itace a saman teburi, amma Chelsea tana taka leda sosai, tare da kyakkyawan salon horarwa, Maresca yayi babban aiki."

🔵 || TAKAITACCIYAR hira da akai da Enzo Maresca jiya kafin wasanmu na gobe da Brentford.Enzo Maresca game lashe kofin Pr...
14/12/2024

🔵 || TAKAITACCIYAR hira da akai da Enzo Maresca jiya kafin wasanmu na gobe da Brentford.

Enzo Maresca game lashe kofin Primier:

🎤"Zaka iya jin hakan [lokacin daka shirya domin lashe kofi, daga abubuwan dana gani a baya], Kana iya jin hakan, kuma watakila shi yasa nace bamu shirya ba, saboda bama ganin hakan kuma bama jin kamshi a wannan lokacin kamar yadda na fada, muna fatan zamu zo gurin nan bada jimawa ba.

Enzo Maresca akan Coach din Brentford Thomas Frank:

🎤"Akaran kansa ban sanshi ba, amma nasan shi tare da tawagarsa tin shekaru da yawa, yana yin babban aiki, yadda suke samun maki, yadda suke taka leda, salo daban-daban da s**a sanya su a kololuwar yanayinsu, hakan abu ne mai kyau."

Enzo Maresca game da mai tsaron raga:

🎤"Maganin ba shine canza mai tsaron raga na farko ba, Amma a wannan yanayin muna da masu tsaron raga biyu masu kyau, Idan s**a ci gaba da kiyayewa a matsayi iri ɗaya, toh muna farin ciki da hakan."

Enzo Maresca game da Jackson:

🎤“Nico ya kasance a takure cikin fushi saboda bai zura kwallo a raga ba, amma Ni a gareni Nico ne yayi abu mafi muhimmanci a wasan, yayinda muka chi kwallon Drow 2-2, gaba daya kowa yana murna, amma Nico shine dan wasa kadai da yaje gun kwallon ya mayar da ita cikin sauri tsakiyar fili domin ci gaba da wasa, hakan zai nuna maka Jackson yana son ayi nasara, wannan shine yanayi mafi mahimmanci a wasan.”

Enzo Maresca:🎤 "Muna buƙatar magoya bayanmu ranar lahadi [Chelsea Vs Brentford] muna buƙatarsu a bayanmu domin ina jin wasan zai kasance mai wahala..”

Wannan shine kadan daga cikin mahimman amsoshi da Enzo Maresca ya amsa a taron manema Labaran jiya

Let’s go Blue
Chelsea Hausa fans🔵

Address

Yankaba
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Labaran Chelsea A Hausa II posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category