17/09/2025
SHEKARUN FARKOFARKO NA TASHEN BALAGA GA YARANMU, ME YAKAMATA MUYI?
Gudunmowar Umar Abdullahi Darmanawa primary Kano
Kwanan-Wata: 17-09-2025
↪️ Daga lokacin da yara s**a kai matakin tashen balaga wato "Early Adolescence Stage" daga shekaru 12, 13, 15 zuwa 18, to wannan shi ne lokaci mafi hatsari ga su yaran da iyayensu;
↪️ A lokacin ne yara suke zama Nagari ko Na-banza, masu amfanar da al'umma ko masu cutar da su;
↪️ Yara sun fi tasirantuwa da abokai ko kawaye fiye da malamai ko iyaye;
↪️ Yara suna jin daidai suke da kowa a duniya, kuma zasu iya yin komai k**ar yadda kowa yake yi;
↪️ A lokacin ne yaro yake neman 'yanci daga ikon iyaye akansa. Yana son dakinsa daban, wajen kwanciyarsa daban, abinci daban, sutura daban, su aski da gyaran jiki sai wanda ransa yake so;
↪️ A lokacin ne yake jin karfinsa ya kawo, kuma zai iya ja da kowa;
↪️ A lokacin yaro komai yana yin sa ne gaga-gaga da zafin-kai, ba kan-gado babu nutsuwa, kuma ba wanda ya isa ya hana shi (a tunaninsa). Idan kuma iyaye ba su bi hanyar da ta dace ba, to za su sha wahala da shi da ita;
↪️ A daidai wannan lokacin ne tsananin sha'awar ke sanya yaro ko yarinya su shiga layin Assha da Fasikanci idan ba dagaske akayi da kula da yawaita addu'a ba, musamman daga Iyaye ko masu kula dasu;
↪️ A daidai wannan lokacin, gaasa zata soma shiga ransa yadda zaiso yayi rayuwar jindadi irin ta sa'anninsa. Idan ba'ayi da gaske ba sai ya soma kokarin nemo kudi ta kowanne hali;
↪️ A daidai wannan lokaci, zai soma kokarin watsi da tsoffin abokai ya soma nemo sabbi wa'yanda ra'ayi yazo daya - nagari ko gurbatattu. Zai rage yawan zaman gida, yana yin nesa da unguwa inda aka saba ganinsa akai-akai.
MAFITA DA SHAWARWARI 👇
🔥1. Iyaye su ja 'ya'yansu a jiki, kuma su yi amfani da hikima wajen yi musu gyara da tarbiyya. Su ninninka sanya musu idanu kwarai kwarai;
🔥 2. Sanya yaro ko yarinya a makarantar da ake karantar da boko da addini. Karatun Boko zalla babu na Addini shi yakesa mu cikin fadawa hannun shuwagabanni mar