19/10/2026
RANGERS TA KAI ƘORAFI GA CAF KAN ABIN DA YA FARU A ABEOKUTA
Ƙungiyar Rangers International FC ta Enugu ta tabbatar da cewa ta kai ƙorafi a hukumance ga Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika (CAF), kan abubuwan da s**a faru da magoya bayan MC Alger a wasan CAF Champions League a filin wasa na MKO Abiola a ranar Lahadi, 18 ga Oktoba, 2026.
A cikin ƙorafin nata, Rangers ta bayyana damuwa kan:
- Rushe ƙofar shiga filin wasa.
- Shiga filin wasa ba tare da biyan kuɗin tikiti ba.
- Lalata kujerun filin wasa da kuma wasu rikice-rikice.
Rangers ta buƙaci CAF da ta gaggauta binciken lamarin tare da ɗaukar matakan da s**a dace kafin wasan dawowa da za a buga a Algiers ranar Juma'a, 23 ga Oktoba, 2026.
Ƙungiyar ta jaddada cewa tana ci gaba da bin doka da oda, tare da ba da muhimmanci ga tsaron 'yan wasa da magoya baya, kuma tana da yaƙinin cewa CAF za ta ɗauki matakin da ya dace.
JMH Sports Update