Kwallo

Kwallo A wannan page zamu din ga kawo muku labaran wasanni da dumi dumin su

Real Madrid za ta bada fam miliyan 130 kan Olise, RB Leipzig za ta rike DiomandeReal Madrid za ta yi wa Bayern Munich ta...
06/06/2026

Real Madrid za ta bada fam miliyan 130 kan Olise, RB Leipzig za ta rike Diomande

Real Madrid za ta yi wa Bayern Munich tayin fam miliyan 130 kan dan wasan Faransa Michael Olise, mai shekara 24, idan aka zabi Florentino Perez a matsayin shugaban kungiyar.(Telegraph - subscription required), external

Tsohon kocin Liverpool Arne Slot, da kungiyar ta kora a makon daya gabata, ya yi watsi da damar rike ragamar horar da 'yan wasan kungiyar Fulham bayan da Marco Silva ya sanar da cewa zai bar kungiyar ta landan. (Talksport), external

Yunkurin da Barcelona ke yi na sayan dan wasan Argentina Julian Alvarez ya gamu da cikas kuma Atletico Madrid na shirin saka sunansa a cikin jerin 'yan wasan da za su yi wasa a kaka mai zuwa, ya yin da Arsenal ita ma ta na sha'awar daukarsa, sai dai ba ya son ya koma Landan (Cadena Ser - in Spanish), external

Watakila dan wasan Chelsea da Ingila Liam Delap, mai shekara 23, ya koma Fulham idan tsohon kocinsa a Ipswich Town, Kieran McKenna, ya maye gurbin Marco Silva a Craven Cottage. (Talksport), external

Tsohon kocin Crystal Palace Oliver Glasner ya fi kocin tawagar Amurka Mauricio Pochettino damar zama sabon kocin AC Milan. (Gazzetta dello Sport - in Italian), external

Dan wasan AC Milan Rafael Leao, mai shekara 26, ya ce yana bukatar sabon wuri, inda dan wasan kasar Portugal ya yi ammanar cewa koma wa gasar wasan Premier League ko La Liga zai dace da shi . (Sport TV, via Football Italia), external

Kawo yanzu RB Leipzig tana da kwarin gwiwar cewa dan wasan gaban Ivory Coast Yan Diomande, mai shekara 19, zai ci gaba da zama a kungiyar a bazarar nan duk da kokarin da Liverpool ke yi domin daukarsa.(Teamtalk), external

Newcastle United na shirin sanya hannu kan cinikinta na farko a wannan bazara bayan sun amince da yarjejeniyar fam miliyan 24 kan mai tsaron ragar Faransa Reims Ewen Jaouen mai shekaru 20.(Northern Echo), external

Kocin Tottenham Roberto de Zerbi na son dan wasan Croatia Luka Vuskovic mai shekara 19 ya bar kungiyar a wannan bazara . (Football Insider), external

Barcelona za ta sayi Marc Cucurella, mai shekara 27, daga Chelsea idan ta yanke shawarar sayarda dan wasan Sfaniya Alejandro Balde, mai shekara 22, a wannan bazara (Marca - in Spanish), external

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

Liverpool da PSG na zawarcin Diomande,AIK Stockholm na son YohannaLiverpool ta kara kaimi a zawarcin da ta ke yi wa dan ...
05/06/2026

Liverpool da PSG na zawarcin Diomande,AIK Stockholm na son Yohanna

Liverpool ta kara kaimi a zawarcin da ta ke yi wa dan wasan Ivory Coast Yan Diomande ta hanyar tuntubar kungiyar RB Leipzig ta kasar Jamus, wacce ba ta son ta sayar da dan wasan mai shekara 19. (Athletic - subscription required), external

Ita ma Paris St-Germain ta nuna sha'awar daukar Diomande din , wanda ya ce ya fi son komawa kungiyar ta Faransa (Telefoot, via Mirror), external

Arsenal na fuskantar hamayya daga Paris St-Germain a yunkurin dauko dan wasan Faransa Eli Junior Kroupi, mai shekara 19, daga Bournemouth da dan wasan Argentina Julian Alvarez, mai shekara 26, daga Atletico Madrid.(Independent), external

Brentford ta yi wa dan wasan Cologne na kasar Jamus Said El Mala mai shekara 19 tayin yuro miliyan 50. (Bild - in German), external

Sai dai, El Mala ya fadawa Brentford cewa ba ya son ya koma taka leda kungiyar da ke wasan firimiya. (Sky Sports Germany), external

Dan wasan Chelsea Marc Cucurella,mai shekara 27, na nazarin barin Stamford Bridge, ya yin da Atletico Madrid ke shirin zawarcin dan wasan kasar Sfaniya . (Teamtalk, external)

Juventus na son akalla kudi yuro miliyan 30 akan dan wasan Italiya Andrea Cambiaso, mai shekara 26 wanda Chelsea da Barcelona ke harinsa. (Calciomercato - in Italian), external

Dan wasan kasar Serbia Dusan Vlahovic zai bar Juventus idan kwantagarinsa ya zo karshe a karshen wata Yuni bayan da dan wasan mai shekara 26 ya yanke shawarar kin rattaba hannu kan sabuwar yarjejenya da kungiyar ta Italiya. (Football Italia), external

Juventus ta sake nuna sha'awar dauko dan wasan Crystal Palace da Faransa Jean-Philippe Mateta, mai shekara 28, kuma su na son dan wasan Atletico Madrid da Norway Alexander Sorloth, mai shekara 30. (Gazzetta dello Sport - in Italian), external

AIK Stockholm suna tattaunawa da dan wasan Nijeriya Zadok Yohanna mai shekara 18 wanda Brighton da Chelsea da kuma Newcastle United ke zawarcinsa. (Northern Echo), external

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

Man City da Chelsea na son Cambiaso, Barca za ta riƙe RashfordManchester City da Chelsea na son dan baya na gefe na Juve...
03/06/2026

Man City da Chelsea na son Cambiaso, Barca za ta riƙe Rashford

Manchester City da Chelsea na son dan baya na gefe na Juventus Andrea Cambiaso, kamar yadda ita ma Barcelona ke sa ido a kan dan tawagar ta Italiya mai shekara 26. (Gazzetta dello Sport)

Kungiyoyin Bayern Munich da Arsenal na sha'awar sayen dan bayan Eintracht Frankfurt ta Jamus Nathaniel Brown, mai shekara 22. (The Athletic)

Aston Villa na sane da sha'awar da kungiyoyi da dama ke nunawa a kan danwasanta na tsakiya Morgan Rogers. Kungiyoyin da s**a hada da Arsenal, amma kuma ba ta da niyyar sayar da danwasan na tawagar Ingila mai shekara 23. (Telegraph)

Watakila Liverpool da Paris St-Germain su nemi sayen danwasan gaba na gefe na RB Leipzig Yan Diomande amma kuma kungiyar ta Jamus ba ta nuna wata damuwa ba a kan lamarin kasancewar ta yi amanna matashin mai shekara 19, ba kawai zai so ya kara shekara daya ba a kungiyar, zai ma rattaba hannu a kwan wani sabon kwantiragin da ya fi na da armashi. (Sky Sports)

Kociyan Barcelona Hansi Flick, da darektan wasanni Deco da kuma shugaban kungiyar Joan Laporta har yanzu suna sha'awar rike dan gaban Manchester United Marcus Rashford da ke zaman aro a kungiyar ya zama na dindindin, yayin da Bayern Munich, da Newcastle, da Tottenham da kuma Aston Villa ke nuna sha'awarsu a kan dan tawagar ta Ingila mai shekara 28. (The I)

Juventus na duba yuwuwar sayen dan gaban Bournemouth da tawagar Netherlands Justin Kluivert mai shekara 27, a madadin Brahim Diaz na Real Madrid da Morocco, mai shekara 26. (Gazzetta dello Sport)

Manchester United na zawarcin dan bayan Juventus da Faransa Pierre Kalulu, kuma kila kungiyar ta Italiya ta sayar da danwasan mai shekara 25, bayan da ta kasa samun gurbin zuwa gasar Zakarun Turai. (Corriere dello Sport)

An bai wa danwasan tsakiya na Portugal Mateus Fernandes, mai shekara 21, damar barin West Ham bayan Manchester United da Arsenal, sun yi tuntuba a kansa, yayin da ita ma Liverpool da Paris St-Germain suna sa ido a kan makomarsa. (Teamtalk)

Aston Villa, da Atletico Madrid da Borussia Dortmund na sha'awar dan gaban Club Brugge, na Jamus Nicolo Tresoldi, mai shekara 21, bayan tashen da ya yi a Belgium a kakar da ta kare. (The Athletic)

Real Madrid ta tattauna da dan bayan Inter Milan Denzel Dumfries, wanda kwantiraginsa ya tanadi sayar da shi a kan fam miliyan 21.6, a yunkurin da kungiyar ta Sifaniya ke yi na ganin ta sayi dan tawagar Netherlands mai shekara 30 a matsayin babban wanda za su saya domin karfafa bayansu. (Athletic)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

Inter Miami na son Guardiola, Silva zai koma BarcelonaAn wallafaAkwai rashin tabbass game da makomar Marc Cucurella a Ch...
02/06/2026

Inter Miami na son Guardiola, Silva zai koma Barcelona
An wallafa

Akwai rashin tabbass game da makomar Marc Cucurella a Chelsea bayan da kungiyoyi da dama s**a tuntubi wakilan dan wasan kan barin Stamford Bridge. An ce Atletico Madrid da Barcelona da kuma Real Madrid na daga cikin wadanda ke zawarcin dan wasan na Sifaniya mai shekara 27.(The Athletic - subscription required), external

Liverpool na zawarcin dan wasan RB Leipzig Yan Diomande amma har yanzu ba su cimma matsaya ta baki ba kan cinikin dan wasan na Ivory Coast mai shekara 19. (Sky Sports), external

Newcastle ta bayyana dan wasan bayan Atalanta na Italiya Marco Palestra, mai shekara 21, a matsayin babban dan wasan da take son ta saya a bazara amma za ta iya fuskantar hamayya daga Manchester City da Arsenal da Inter Milan. (Mail), external

Daya daga cikin mutanen da s**a mallaki Inter Miami, David Beckham na son ya dauki Pep Guardiola aiki a matsayin sabon kocin kungiyar ta Major League Soccer bayan ya bar Manchester City, sai dai dan kasar Sifaniya zai yi watsi da duk wani tayi na komawa filin wasa nan take.(Mirror), external

Dan wasan Portugal Bernardo Silva na shirin rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyu da Barcelona bayan ya bar Manchester City kuma dan wasan mai shekara 31 yana son a kammala cinikin a hukumance kafin karshen mako.(AS - in Spanish), external

Watakila dan wasan Ingila Marcus Rashford, mai shekara 28, ya koma Manchester United a shirye-shiryen kakar wasa ta bana, yayin da komawarsa Barcelona, ​​inda ta kasance aro a kakar wasan da ta gabata, ta gamu da cikas.(Times - subscription required), external

Manchester United na son ta cefanar da Rashford domin taimaka wa sabon kocin kungiyar Michael Carrick' samun kudin musayar 'yan wasa kuma Arsenal da Chelsea da Newcastle da Tottenham na bibiyar halin da ake ciki . Kungiyar dai ba ta son ta sayar da dan wasan ga daya daga cikin manyan abokan hammayarta. (Mirror), external

Nottingham Forest za ta tattauna da dan wasan tsakiya Ibrahim Sangare, mai shekara 28, kan sabon kwantaragi yayin da Manchester United da Besiktas ke zawarcin dan kasar ta Ivory Coast.(Football Insider), external

Dan wasan kasar Ivory Coast Evann Guessand, mai shekara 24, na nazari kan kungiyar da zai koma bayan karewar wa'adin aronsa daga Aston Villa zuwa Crystal Palace don mayar da cinikin na dindindin .(Evening Standard), external

Aston Villa na son ta bar dan wasan Sifaniya Andres Garcia, mai shekara 23, barin kungiyar a matsayin aro a lokacin bazara, inda Valencia da Elche na cikin cikin kungiyoyin da ke zawarcinsa. (Tribuna Deportiva - in Spanish), external

Tottenham ta bayyana dan wasan Eintracht Frankfurt Jean-Matteo Bahoya a matsayin dan wasan da take son ta saya, amma kungiyar ta Bundesliga ba za ta bar dan Faransa mai shekara 21 ya tafi a farashi mai rahusa ba.(Teamtalk), external

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

Arsenal da PSG na zawarcin Rogers, Alisson zai koma JuventusKocin Arsenal, Mikel Arteta, ya nuna aniyar dauko dan wasan ...
01/06/2026

Arsenal da PSG na zawarcin Rogers, Alisson zai koma Juventus

Kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya nuna aniyar dauko dan wasan Aston Villa da Ingila Morgan Rogers, mai shekara 23, a kokarinsa na ci gaba da samun nasarar lashe gasar Premier, duk da cewa Paris St-Germain da ta lashe gasar zakarun Turai ita ma na zawarcinsa. (Mirror), external

Manyan masu daukar ma'aikata a Real Madrid sun bukaci kungiyar ta nemi dan wasan Arsenal Declan Rice, sakamakon yadda dan wasan na Ingila mai shekaru 27 ya burge su kan jagoranci da kuma kwarewa.(Teamtalk), external

Golan Liverpool Alisson, mai shekara 33, yana shirin fada wa sabon kocin kungiyar cewa yana son ya bar Anfield ya koma Juventus. (Gazzetta dello Sport - in Italian), external

Manchester United na gab da kulla yarjejeniya da dan wasan Brazil Ederson, mai shekara 26, daga Atalanta kan kudi kusan fan miliyan 35. (Talksport), external

Dan wasan Portugal Joao Palhinha, mai shekara 30, ba ya son aron da aka ba da shi daga Bayern Munich zuwa Tottenham ya koma na dindindin kuma zai yi kokarin ganin ya koma Sporting a maimakon haka. (A Bola - in Portuguese), external

Manchester United da Chelsea da Arsenal da Tottenham da Liverpool da kuma Newcastle dukkaninsu na zawarcin dan wasan AC Milan da Portugal Rafael Leao inda dan wasan mai shekara 26 na son ya bar San Siro a wannan bazara . (Calciomercato - in Italian), external

Paris St-Germain ta fasa daukar dan wasan Atletico Madrid Julian Alvarez, sai dai dan wasan Argentina mai shekara 26 na jan hankalin Arsenal da Barcelona. (Mundo Deportivo - in Spanish), external

An yi wa Inter Milan tayin dan wasan Manchester United Harry Maguire sai dai kungiyar ta Italiya ba ta dauki daukar dan wasan Ingila mai shekara 33 a matsayin wani abu da za ta ba fifiko ba (Gazzetta dello Sport via Football Italia), external

Dan wasan Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31, yana sha'awar komawa Barcelona ya yin da kwantiraginsa a Manchester City na gab da karewa.(Mundo Deportivo - in Spanish), external

Brighton za ta fuskanci hamayya daga Hoffenheim da Eintracht Frankfurt wajan sayen dan wasan Wolfsburg Patrick Wimmer mai shekaru 25 .(Florian Plettenberg), external

Crystal Palace ta sake tattaunawa da kocin Lens Pierre Sage da ake ganin yana da kwarewa sosai .(Mail), external

Kocin Como Cesc Fabregas na jin dadin aikinsa a kungiyar Italiya duk da cewa an alakanta da shi da wasu ayuikam horas dayan wasa a wasu wurare ciki harda Real Madrid (Sport - in Spanish)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

AC Milan na son Glasner a matsayin kocinta, Newcastle na zawarcin EzzalzouliTsohon kocin Crystal Palace Oliver Glasner n...
31/05/2026

AC Milan na son Glasner a matsayin kocinta, Newcastle na zawarcin Ezzalzouli

Tsohon kocin Crystal Palace Oliver Glasner na shirin tattaunawa da AC Milan kan mukamin kocin kungiyar bayan sallamar da ta yi wa Massimiliano Allegri.(Mail), external

Bayern Munich na zawarcin dan wasan Bournemouth da Faransa Junior Kroupi, mai shekara 19, a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan Colombia Luis Diaz a lokacin wasa . (Absolut Bayern via Merkur - in German), external

Liverpool da Inter Milan suna tattaunawa kan cinikin dan wasan Ingila Curtis Jones, mai shekara 25, amma Liverpool ta fi son a ba ta kudi fiye da yuro miliyan domin ta sayar da dan wasan.(Fabrizio Romano)

Dan wasan Brazil da Galatasaray, Gabriel Sara mai shekara 26 ya maida martani mai kyau ga Aston villa da ke zawarcinsa. (Sabah - in Turkish), external

Chelsea na sha'awar dan wasa mai kai hari Mikkel Bro Hansen, mai shekara 17 wanda kwanragarinsa a Bodo/Glimt zai zo karshe a 2027, sai dai Newcastle da Manchester City sun sa ido kan matashin dan kasar Denmark. (Caught Offside), external

Sporting na tunanin bada aron dan wasan Girka da Everton Georgios Vagiannidis mai shekara 24 (A Bola - in Portuguese), external

Chelsea ta yanke shawarar dakatar da tayin da za ta yi wa dan wasan Liverpool wanda zai bar kungiyar, Ibrahima Konate mai shekara 27 kuma wakilan dan kasar Faransa na tattaunawa da wakilan Real Madrid da Bayern Munich.(Teamtalk), external

Juventus na bibiyar tsohon golan Manchester United da Sfaniya,David de Gea, mai shekara 35 wanda shi ne golan Florentina. Goal), external

Preston North End ta yanke shawarar siyan dan wasan Tottenham Alfie Devine a tattaunawar ba da shi aro kuma a shirye suke su kafa tarihi a musayyar da suke son su yi kan dan wasan Ingila mai shekara 21. (Lancashire Post), external

Dan wasan Moroko da Real Betis Abde Ezzalzouli mai shekara 24, ya bayyana a matsayin wanda watakila zai maye gurbin tsohon dan wasan Newscastle AnthonyGordon inda Tottenham da Aston Villa ke zawarcinsa. (Sport - in Spanish)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

Atletico Madrid na zawarcin Tijjani, Silva ya fi son ya koma BarcelonaAn wallafaDan wasan AC Milan da Portugal Rafael Le...
30/05/2026

Atletico Madrid na zawarcin Tijjani, Silva ya fi son ya koma Barcelona
An wallafa

Dan wasan AC Milan da Portugal Rafael Leao, mai shekara 26, na cikin jerin 'yan wasan da Manchester United ke zawarcinsu kuma za a same shi kan farashi mai rahusa bayan kungiyar ta Italiya ta kasa tsallakewa zuwa gasar zakarun Turai.(Football Insider), external

Dan wasan Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31,zai kasan ce ba shi da kwantaragi bayan ya bar Manchester City a wannan bazara kuma Atletico Madrid da Benfica sun yi masa tayi amma ya fi son ya koma Barcelona.(Times, subscription required), external

Dan wasan Eintracht Frankfurt Jean-Matteo Bahoya, mai shekara 21, na jan hankalin kungiyoyin kwallon kafa na firmiya da Turai yayin da kungiyoyin Saudi Pro League suma suna zawarcin dan wasan na Faransa na tawagar yan kasa da shekara 21.(Sky Sports, external)

Kocin Jamus Dino Toppmoller, wanda ya bar kungiyar Frankfurt ta Bundesliga a watan Janairu, yana daya daga cikin 'yan takarar da za su maye gurbin Oliver Glasner na Austriya, mai shekara 51, a Crystal Palace.(Sky Sport - in German, external)

Aston Villa na tattaunawa da dan wasan tsakiyar Netherlands Lamare Bogarde, mai shekara 22, kan sabon kwantaragi don ya ci gaba da taka leda a kungiyar.(Football Insider), external

Tsohon kocin Bournemouth Andoni Iraola na tattaunawa da Bayer Leverkusen ta Bundesliga kan zama kocinsu.(Times, subscription required), external

Barcelona da Bayern Munich na zawarcin dan wasan bayan Manchester City da Croatia Josko Gvardiol, mai shekara 24(Goal), external

Atletico Madrid na shirin neman dan wasan Manchester City da Netherlands Tijjani Reijnders, mai shekara 27, wanda ya koma kulob din na Ingila a bazarar da ta wuce.(Daily Mail)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

Barca za ta dauke wa Arsenal Hincapie, Man U da Chelsea na neman ScottBarcelona na nazarin yiwuwar daukar dan wasan baya...
29/05/2026

Barca za ta dauke wa Arsenal Hincapie, Man U da Chelsea na neman Scott

Barcelona na nazarin yiwuwar daukar dan wasan baya na Arsenal kuma dan ƙasar Ecuador, Piero Hincapie mai shekara 24. (Mail)

Dan wasan baya na Manchester City kuma dan ƙasar Portugal, Ruben Dias mai shekara 29, ya umarci wakilansa su fara duba yiwuwar barinsa kungiyar, inda Paris Saint-Germain da Bayern Munich da kuma Real Madrid ke sa ido kan halin da yake ciki. (Caught Offside)

Liverpool na kokarin cimma yarjejeniya cikin gaggawa da dan wasan gefe na RB Leipzig, Yan Diomande, yayin da Paris Saint-Germain da Manchester City s**a fara tattaunawa da dan wasan na Ivory Coast mai shekara 19. (Florian Plettenberg)

Crystal Palace na son shawo kan dan wasan tsakiyar Ingila Adam Wharton mai shekara 22 da kuma dan wasan Japan Daichi Kamada mai shekara 29 su ci gaba da zama a kungiyar bayan nasarar da s**a samu a wasan karshe na Conference League. (Sky Sports)

Bournemouth na kokarin dakile duk wani tayi a bazara kan matashin dan wasan gaba na Faransa Eli Junior Kroupi mai shekara 19, da dan wasan gefe na Brazil Rayan mai shekara 19, da kuma dan wasan tsakiyar Ingila Alex Scott mai shekara 22, saboda yadda kungiyoyi da dama ke nuna sha'awa a kansu. (Guardian)

Leeds United na shirin zawarcin dan wasan tsakiyar Lyon kuma dan Amurka Tanner Tessmann mai shekara 24 a wani bangare na harkokin saye da sayarwa da kungiyar ke shirin yi a bazara. (Football Insider)

Manchester City na nazarin matakin da za ta dauka idan dan wasan gefe na Brazil Savinho mai shekara 22, wanda Tottenham ke sha'awar dauka, ya bar kungiyar. (Fabrizio Romano)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

Arsenal ta sa Jesus a kasuwa, City ta dage kan AndersonAn wallafaArsenal ta yi wa danwasanta na gaba Gabriel Jesus, dan ...
28/05/2026

Arsenal ta sa Jesus a kasuwa, City ta dage kan Anderson
An wallafa

Arsenal ta yi wa danwasanta na gaba Gabriel Jesus, dan Brazil mai shekara 29, farashin fam miliyan 20, ga duk kungiyar da ke son sayenshi a bazaran nan. (Athleti)

Manchester City na bayar da fifiko kan cinikin dan wasan tsakiya na Nottingham Forest da Ingila Elliot Anderson, mai shekara 23, yayin da take shirin fuskantar rayuwa bayan Pep Guardiola. (Mail)

Amma kuma City din ba ta da sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Chelsea Enzo Fernandez, na Argentina mai shekara 25, wanda ke son barin kungiyar ta Stamford Bridge. (Sky Sports)

RB Leipzig ta nuna cewa danwasanta na gaba na gefe Yan Diomande, na Ivory Coast mai shekara 19, wanda Liverpool, ke so ba inda za shi a bazaran nan, bayan da kungiyar ta amus ta samu gurbin zuwa gasar Zakarun Turai ta kaka mai zuwa. (Mirror)

Bayer Leverkusen na fatan shawo kan kociyan Bournemouth mai barin gado Andoni Iraola ya karbi aikin sabon mai horad da kungiyar. (Kicker)

Arsenal ta yi kyakkyawan shirin na cinikin danwasan tsakiya na Aston Villa Morgan Rogers na Ingila mai shekara 23. (Football Transfers)

Liverpool na son mai tsaron ragarta Alisson Becker dan Brazil mai shekara 33, ya ci gaba da zama a kungiyar karin kaka daya, wanda hakan ya sa rashin tabbas na shirin golan na tafiya Juventus a bazaran nan. (Gianluca Di Marzio)

Jami'ai daga Liverpool da Inter Milan sun gana a kan cinikin dan wasan tsakiya na Liverpool din Curtis Jones na Ingila mai shekara 25, kan tafiyarsa Italiya. (Gianluca Di Marzio)

A shirye Manchester City take ta saki dan wasanta na gaba na gefe Savinho, dan Brazil mai shekara 22, wanda kuma Tottenham ke sha'awarsa. (Football Insider)

Oscar Mingueza, mai shekara 27, yana son samun kungiya a Firimiya a bazaran nan, kuma, Aston Villa da Newcastle na daga kungiyoyin da suke bin diddigin dan bayan na Celta Vigo dan Sifaniya, wanda zai kasance ba shi da kwantiragin wata kungiya a kansa (Sky Sports)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

An sa hoton ƙwallon da McTominay ya ci Denmark a takardar kuɗin Scotland,ScotlandBankin Scotland ya ƙaddamar da takardar...
26/05/2026

An sa hoton ƙwallon da McTominay ya ci Denmark a takardar kuɗin Scotland,Scotland

Bankin Scotland ya ƙaddamar da takardar kuɗi ta musamman mai darajar £20, wacce ke ɗauke da hoton shahararriyar ƙwallon da Scott McTominay ya ci wa Scotland man ban sha'awa.

An kirkiro wannan takarda ne domin murnar komawar Scotland zuwa gasar FIFA World Cup bayan samu tikitin shiga gasar a karon farko tun bayan shekarar 1998.

Tsarin takardar ya haɗa abubuwan gargajiya na takardun kuɗi tare da hoton kwallon da Scott McTominay ya ci Denmark a wasan neman gurbin shiga gasar.

Takardu 100 kacal aka buga daga wannan nau’i na musamman, inda guda 50 za su kasance ta hanyar gwanjon masu tara kayayyaki, ƙyautar c**a, da kuma wasu wuraren nune-nune a Edinburgh da Glasgow.

Tawagar Scotland ta samu gurbin shiga gasar Kofin Duniya bayan da ta doke Denmark da ci 4-2 a filin Hampden Park a watan Nuwamba.

McTominay ne ya fara cin ƙwallon mai ban mamaki, wacce ta zama daya daga cikin manyan lokutan da s**a taimaka wa Scotland komawa babban matakin ƙwallon kafar duniya.

Ya kuka ganin wannan karramawar?

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kwallo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category