04/09/2026
🚨🔴 Gary Neville ya yi hasashen Arsenal za ta doke Chelsea! 👀
Tsohon ɗan wasan na Manchester United, Gary Neville, ya yi hasashen cewa Arsenal za ta samu nasara a kan Chelsea a fafatawar da za suyi ranar Lahadi a gasar Premier League. 🏆
🔮 Hasashensa: Arsenal 2–0 Chelsea.
Neville ya ce Arsenal na iya samun damar kai hari sosai, amma dole ne ta yi hattara da ’yan wasan gaba masu ƙwarewa na Chelsea.
🔥 Ya kuma bayyana cewa wannan wasan zai kasance babban gwaji ga Arsenal, sannan zai ba da damar ganin yadda Chelsea ƙarƙashin Xabi Alonso take a farkon sabon aikinsa.
🗣️ Neville: “Ina ganin Arsenal za ta yi nasara, amma wannan babban gwaji ne gare ta.”
👀 Toh amma kai mane ne hasashenka? Arsenal ce zata yi nasara ko Chelsea?