02/07/2025
Lissafi ya kwaɓewa Bola Tinubu, dole zai ajiye ƙudirin sa na ɗaukar Kwankwaso a VP 2027.🤣
Yanzu haka jiga-jigan ƴan siyasar Najeriya Kudu da Arewa sun gama haɗuwa waje guda a ƙarƙashin jam’iyyar ADC domin tunkarar Bola Tinubu a zaɓen 2027 mai zuwa.🙆🏻♂️
Bola Tinubu ya k**a hanyar rusa jam’iyyar sa ta APC, sannan yanzu haka ya kawo rikice-rikicen cikin gida a yankin Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da Arewa ta tsakiya sak**akon naɗin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa da kuma yunƙurin sa na ajiye Kashim Shettima a matsayin VP ya ɗauki Rabi'u Kwankwaso.🤣
Ƴaƴan jam’iyyar haɗaka irin su Sule Lamido, Rotimi Amaechi, Abubakar Malami, Peter Obi, David Mark, Aminu Waziri Tambuwal, Rauf Aregbesola, Atiku Abubakar, Nasir Elrufai, Uche Secondus, Babangida Mu’azu, Iyochia Ayu, Fashola Babatunde, Bindow Jibrilla, Ahmed Makarfi sun gama haɗa kan su waje guda, ƙasa ta ɗauki haramar yaƙin neman zaɓen 2027, an fara mitin-mitin. A hannu guda kuma talakan ƙasa ya fusata saboda halin da ya ce gwamnatin Bola Tinubu da APC ta saka shi, don haka jiran umurnin jam’iyyar haɗaka ta ADC kawai ya ke yi.
Jam’iyyar haɗakar nan ta sallama Kwankwaso ga APC, Kwankwaso kuma ba zai iya ciyowa Bola Tinubu Kano ba ma a yanzu yadda talaka ya sha bùgu ballan ta na Arewa maso Yamma.
Shi ma Kashim Shettima da ƴan Arewa maso Gabas sun ɗana tarkon su, a na canja ɗan su Kashim da Kwankwaso sun ja layi.
Mafitar da shugaban ƙasa ya ke shirin ɗauka yanzu shine zai jefar da Kwankwaso, ya rungumi Kashim Shettiman sa, sannan ya miƙawa ƴan Arewa ta tsakiya slot ɗin su na shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa, idan ya so sai ya zo ya fuskanci yadda zai yi winning heart ɗin talakan Najeriya su ƙara zaɓar sa a karo na biyu.🤣🤣
Rabi'u Kwankwaso kuma dole sai dai ya nemi wata jam’iyyar yayi takara shi kaɗai, domin PDP, NNPP, LP, SDP, ADC ta ma su sabuwar tafiyar haɗaka duk sun haƙura da shi. 🤣