30/05/2026
🚨 CIGIYA! ANA NEMAN IYALAN WANI MUTUM DA YA RASU A HATSARIN MOTA A KEBBI
Ana neman ‘yan uwa ko dangin wani bawan Allah da ya rasu bayan ya yi mummunan hatsarin mota a kan hanyar Jega zuwa Argungu a Jihar Kebbi.
Rahotanni sun ce marigayin ya samu munanan raunuka sak**akon hatsarin, inda aka garzaya da shi zuwa Asibitin Tarayya (FMC) da ke Birnin Kebbi domin ceto rayuwarsa. Sai dai duk da ƙoƙarin da likitoci s**a yi, ya rasu bayan isa asibitin.
Kafin rasuwarsa, marigayin ya bayyana cewa shi ɗan Argungu ne. Sai dai babu wata takardar shaida, lambar waya ko wani bayani da zai taimaka wajen gano cikakken sunansa ko danginsa.
A halin yanzu, gawarsa tana ajiye a Asibitin Tarayya (FMC) Birnin Kebbi, yayin da ake roƙon al’umma da su taimaka wajen yaɗa wannan saƙo domin isa ga iyalansa.
Duk wanda ya san wannan mutum ko kuma yana da wani bayani da zai taimaka wajen gano danginsa, a tuntubi waɗannan lambobin waya:
📞 07061307795
📞 08068699091
Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya kuma ba iyalansa damar gano labarinsa cikin sauƙi. Amin.
A taimaka a yaɗa wannan saƙo domin neman iyalansa.
Afr hausa news ©