06/02/2017
GA LITTAFIN ANTY NABILA NA FARKO:
MASOYI ZAKI; A SHA KARATU LAFIYA
“...Yadda za ki gane tauraruwar ki shi ne, ki
kalle su gaba ]aya, ki yi masu kallon tsaf, za ki
ga wacce ta fi dacewa da ke, wacce kika ji ta yi
daidai da ke ruhi da jiki, wacce kika ji ta yi maki
kyau ta kuma dace a ce ta zama tauraruwar ki.
Yanzu ki kalle su ki gano taki ki nuna mani ita!”
Inno ta kalli taurarin nan tsaf. Zuwa can sai ta
yi farat ta nuna wata daga can gafe, ta ce,
“Yaya, ga ta nan!”
Adamu ya kalli wadda ta nuna ]in, sa’annan ya
yi murmushi, ya ce, “Ni kuma kin ga tawa nan
kusa da taki.”
Ita ma ta yi murmushi ta ce, “Allah kuwa,
Yaya?”
Adamu ya sumbanci goshin ta ya ce, “Allah
kuwa, }anwata.” Sa’annan su ka yi dariya tare
da rungume juna. A daidai nan kuma iska mai }
arfi ta taso, aka tsuge da ruwa k**ar da
bakin }warya. Adamu ya ]auke ta su ka shige
cikin bukkar nan, inda a karo na farko su
ka ]an]ani da]in madarar auratayya.
1 MASOYI ZAKI CHAPTER 1
Yau sha tara ga watan Shawwal, Hijira ta na
1491, rana ce ta farin ciki a rayuwar Inno, yau
ne ake daura ma ta aure da babban masoyin
ta, abin kaunar ta, Adamu Zaki.
Adamu abokin wasan ta ne kuma Yayan ta,
domin da Baban ta da mahaifiyar sa uwa daya
uba daya. Haka kuma da Mahaifiyar ta da
Baban sa uwa daya uba daya. Su Inno na zaune
a Gulubba, yayin da shi kuma Adamu su na
zaune a Tumfafi. Duka dai kauyuka ne a yankin
Kwatarkwashi. Kasar Kwatarkwashi gabadayan
ta akan dutse ta ke, watau Dutsen
Kwatarkwashi wanda akan yi wa kirari da
‘Kwatarkwashi dutse da ganuwa.’ Babban garin
karkarar dai Kwatarkwashi ne wanda ya ke a
bakin titin zuwa Gusau, sai Kauyuka ma su yawa
zuzzube manya da kanana. Wasu kauyukan a
kan dutsen su ke, wasu a gindin dutsen, yayin
da wasu su ke kusa da shi. Tsakanin wannan
kauye zuwa wancan bai fi k**ar tafiyar kilomita
biyu ba. Gaba daya al’ummar Kwatarkwashi
manoma ne; Su kan noma gero, dawa, wake,
auduga, da kuma gyada. Auduga; gyada wake
na ci da na suya na sayarwa ne don a samu
abin kashewa, yayin da hatsi akan a je su a
cikin rumbuna don a samu abin ci idan damina
ta kewayo. Manoma kadan ne ke noma masara,
amma su kan noma kubewa da ganye irin su
rama da yakuwa da kuma barkono da tumatir.
Akwai garuruwan Fulani kalilan a yankin; iyayen
Inno da na Adamu asalin su Fulani ne.
Inno kyakkyawar yarinya ce qwarai da gaske;
Shekararun ta goma sha uku;Ta na da
matsakaicin tsawo, da doguwa kuma cikakkiyar
fuska; cikakkiya; Bakin ta dan karami ne, wanda
ya kan fadada idan ta yi murmushi. Hancin ta
dogo ne har baka. Ta na da tsawon gashin kai,
ga shi mai sulbi da taushi. Sa’annan ta na da
irin sajen nan na mata, wanda ya kwanta sulub
a gefen fuskar ta. Akwai kuma wani gashi a
kasan keyar ta, kan kashin da ya hada wuya da
baya. Kalar fatar ta mai kyau ce. Farin Fulanin
asali surki da bakin cakulet. Ta na da irin
murmushin nan mai narkar da zuciya, sa’annan
dariyar ta mai dadi ce da saka nishadi a zuciya.
Amma ba ta yi makarantar boko ba; Ta
Islamiyar ma ba wani nisa ta yi ba, domin ko
izzifi daya ba ta hada ba. Duk da haka, ita irin
yaran nan ne masu son ilmi da wayewa irin ta
zamani. Duk ran da su ka je Gusau ko
Kwatarkwashi tare da Yayar ta wadda ke aure a
wani kauye wai shi ’Yar Tsakuwa, sai Inno ta ji
ina ma a ce ita ma a nan ta ke da zama. Ta na
son kwalliya da sa kaya ma su kyau. Sa’annan
ta cika tunane-tunane iri na soyayya. Kullum in
ta je kiwon shanun gidan su ba abin da take sai
tunane-tunane na soyayya da rayuwar jin dadi
da kwanciyar hankali. Shi ya sa ta na da yawan
samari sosai. Wajen samari takwas su ka kawo
toshi gidan su, cikin su biyar sun kawo gaisuwar
iyaye. Shi ne aka dame ta da ta fitar da daya
da take so domin a daura ma ta aure, sauran
kuma a mayar masu da kayan su. Amma sam
ita ta ki fito da kowa. Ita duk cikin su ba wanda
ta ji ta na so.
Wannan shi ya sa iyayen ta su ka zauna don yin
shawarar wanda ya dace su aura ma ta daga
cikin samarin nan. Amma dai su ka rasa samo
wanda ya k**ata su ba ’yar lelen su. Baban ta
ya na matukar ji da ita sosai don tsananin
ladabi da biyayyar da ta ke da su. Baban na ta
Alhaji Sa’idu babban manomi ne. Mahaifiyar ta
sunan ta na asali Maryama, amma an fi kiran ta
da Meri. Ita ma ta na ji da Inno domin kusan
ita ce kadai ’yar diya macen ta. Tun daga ’yarta
ta fari ba ta kara haihuwar ’ya mace ba sai
Inno bayan ta haifi maza hudu.
Daga karshe dai sai iyayen Inno su ka yanke
shawarar da Alhaji Sa’idu ya je ya tambayi
Alhaji Abu Yayan sa don neman shawarar sa.
Shi kuwa Alhaji Abu, bai yi wata-wata ba ya ce
me zai hana a yi ’yar gida kawai, a hada su da
Adamu tunda shi ma dai auren ya gabace shi
ga shi ya gama makaranta ba ya yin komai sai
zaman gida? Shi ke nan, aka mayar da duk
kayan toshi da na gaisuwar iyaye da aka kawo.
Aka sa ranar daurin auren Adamu da Inno.
Inno ta yi mamaki da ta ji an sa ma ta rana da
Adamu. Ita ba ta taba tunanin za ta aure shi
ba. Ita dai ta fi daukar sa a matsayin Yayan ta.
Duk Yayyenta a abokin wasa su ke daukar sa,
haka kuma kannen ta. Ba k**ar mai bi mata,
wacce su ke uba daya da Innon, ta raina shi
sosai, kuma ko a ina ne sai ta tsokane shi. Inno
kadai ce mai daraja shi har ta kira shi Yaya. Shi
ya sa su ke shiri sosai da shi. Duk inda ya gan
ta sai ya yi ma ta kyauta. Yadda ya ke ma ta ko
kannen shi mata bai ma haka. Kuma duk
lokacin ta ta je gidan su ta yi kwanaki duk abin
da ta ke so zai ma ta shi. Lokacin ta na karama,
ya na dora ta a kan jaki ya na bayan ta su yi ta
yawo cikin gari. Sannan ya na dora ta a kan
wuyan sa ya yi ta yawo da ita, ita kuwa ta na
dariya. Idan ta na wasan tuwon kasa kuwa sai
ya yanka ma ta tantabara da ya ke ya na kiwon
su da yawa ta yi miya da ita. In ta gama ta
zuba ta kawo ma sa, shi kuwa ya yi k**ar ya na
ci ya ce bai taba cin abincin da ya yi dadin na
ta ba. Haka in ta na wasan carafke ya na zama
su dinga yi tare. In kuma za shi yawon farauta
cikin dutse wata sa in ya kan dauke ta su je
tare, su kan debo kanya ko baure. Wata sa’a
kuma zai sami harbe wani naman dawa ya zo
ya gasa ma su su ci. In lokacin damina ne kuwa,
kullum tare su ke zuwa gonar sa in ya yi noma
ta yaye masa ciyawar ta zuba a buhu don a je
da ita gida a ba awaki da tumaki. In Kaka ta zo
kuma ta na zuwa gonar sa ta na taya shi roron
wake da tabin (ko dibar) kada. In kuma gyada
ce, in ta sheke ma sa buhu ukku sai ya ba ta
daya. Ya na da gonaki hudu ne, kuma duk shi
yake nome abin sa. Duk cikin dangin su ba
wanda ya yi makarantar gaba da firamare ya
kare sai shi. Ga shi kuma ya iya gayu sosai irin
na ’yan birni. Ita dai ana cewa an sa ma ta
rana da Yaya Adamu sai ta ji a ko da yaushe ta
na yawan tunanin sa. Sai ta ji son sa ya cika
zuciyar ta. Kullum abubuwan da su ka yi tare ne
ke cika zuciyar ta. Amma abin mamaki shi sam
yanzu ba ya kula ta sosai, ko ya zo, iyaka ya yi
ta hira da Umma. Amma ita sai ya yi shiru da
ita. Rabon da ya yi hira sosai da ita tun
daminar bara waccan, lokacin ta je can wajen
bikin sunan Yayan Adamun da matar sa ta
haihu. Bayan an watse taron suna sai Umma
Danejo, Innar Adamu ta ce ta tsaya ta yi ma ta
sati a can. Rannan ta je kiwon shanu cikin
dutse, da ma kauyen Tumfafi a gindin dutse ya
ke. Da yamma ta yi sai ta kora shanu gida ta
sha fura sannan ta koma cikin dutse ita da
kannen Adamu ’yan mata don su debo kanya.
Bayan sun debi kanyar sai Azeema ta ce su je
rafi su yi wanka. Da man akwai kwari a falefalen
dutse wanda ke cika da ruwa lokacin damina.
Kowaccen su ta na da rigar leda wadda su ka
sanya su ka tsunduma cikin ruwa su uku, su na
ta iyo su na fancan-fancan a cikin ruwa. Su kan
fito su hau wani mulmulen dutse da ke kusa da
rafin su yi tsaye sa’anan su fada ciki fanjam. Su
Azeema da Hassana su ka fita su ka zauna su
na duban arewa. Ita kuwa Inno ta haye kan
mulmulen dutse ta na duban yamma inda rana
ta yi ja wur ta kusa faduwa. Azeema da
Hassana su ka sanya kayansu s**a ce, “Inno,
tashi mu tafi gida.”
“Ku tafi ina zuwa sai rana ta shige bayan dutse
tukunna.” In ji Inno, su ka yi tafi su na tonon ta
cikin dariya da sai kura ta zo ta cinye ta.
Ta sanya kayan ta ta sake hawa mulmulen
dutsen nan, ta na ta kallon rana a hankali ta na
shigewa bayan dutse. Can ta yi rabi sai ta
hango wani a kololuwar dutsen ya na gittawa
da karnukan farautarsa a baya. Ya na zuwa
saitin da ranar ta rabu biyu sai ya tsaya ya na
duban ranar, ya dora hannuwan sa a kugun sa,
ga karnukan sa sun sa shi a tsakiya, da ya irin
tsayuwar da ya yi ta gane ashe Yaya Adamun ta
ne. Ita kuwa sai ta ji a ran ta da ma ta na da
abin daukar hoto, lallai da ta dauke shi hoto a
wannan lokacin. Amma duk da haka, ta ajiye
hoton a can cikin ma’adanar zuciya, iyaka duk
lokacin da ta yi marmari ta fito da shi ta kalla
da kwayar idon zuciyar ta. Sai da ranar ta rage
kadan ta bace sannan ya gangare daga kan
kololuwar dutsen. Ita kuma ta na nan zaune ta
na kallon baiwa da ikon Ubangiji har ranar ta
bace gabadaya, sai gajimare kawai tare da
wasu gizai-gizai, ta nsa nan har su ka karasa
bacewa. Ita dai sarauta da girman iko irin na
Ubangiji ya na girgiza ta tare da ba ta mamaki;
idan ba shi ba wanene ke da ikon wanzar da
al’amarin tafiyar rana da kuma fitowar wata?
Ita kam da za ta iya da ta fito da asubar fari
domin ta ga yadda rana za ta juyo ta sake
fitowa ta gabas bayan ta fadi a yamma
Ta na nan ta tsunduma cikin tunani sai, ba zato
ba tsammani, ta ji wata kara mai k**a da
gurnanin zaki a saitin kunnen ta. Haba, nan da
nan ta razana ta sulale daga kan dutsen ta na
niyyar fadowa. Amma sai ta ji ta an tallabe a
wasu irin karfafan hannuwa; sa’annan ta ji an
kyalkyace da dariya mai cike da jin dadi da
annashuwa. Ta na dubawa sai ta ga ashe Yaya
Adamu ne ya tsorata ta. Duk kunya ta k**a ta.
Shi kuwa ya ajiye ta ya na murmushi, ka na ya
ce, “Ashe kina da tsoro haka Fatima?” Duk
duniyar nan shi kadai ke kiran ta da sunan ta na
gaskiya, kowa Inno ya ke ce ma ta.
Ta rufe ido don kunya, sa’annan ta ce, “Kai
Yaya Adamu, ba kyau fa ba dan’uwa tsoro!”
“Yi hakuri Kanwa ta. Amma na dade da zuwa
nan, sam ba ki san na zo ba. Me k**e tunani
ne?”
“Ni ba na tunanin komai. Ina dai kallon faduwar
rana ne.”
“Ashe sha’awar mu daya da ke. Gobe zan tayar
da ke da asuba mu zo mu yi kallon fitowar
rana.”
“Lah, Yayah! Kamar ka san ina matukar son in
zo in ga rana ta na fitowa. Don dai ba zan iya
zuwa ni kadai ba ne, kuma na san su Azeema
ba za su rako ni ba.”
Daga nan s**a juya don zuwa gida. Adamu ya
ce a yi tsere, in ta riga shi zai je da ita yawon
farauta. Tun tuni ta ke son ya bar ta ta kara
raka shi yawon farauta amma ya ki; tun da ya je
da ita sau daya bai kara zuwa da ita ba. Don
haka ta dage ta ruga da gudu ta wuce shi. Har
ta isa gangaren dutsen ke nan sai kafarta ta
karkace ta fadi kasa ruf-da-ciki. Nan da na
Adamu ya yi sauri ya dauke ta, ya na ta,
“Sannun Inno, sannu ‘yar kanwata, kar ki kuka
kin ji!”
Ta gurje a kunci kuma ta buge kan ta har
goshin ya kumbura, sa’anan ta yi targade a
kafa. Ya goya ta, su ka karasa gida. Su na zuwa
gida ya aje ta a kan tabarma.Umma Danejo ta
ce, “Lafiya? Me ya same ta?”
“Faduwa ta yi,” inji Adamu. Ya na dariya ya ci
gaba ya yi mata bayanin yadda abin ya faru.
Ta ce a cikin hassala: “Wai kai Adamu me ya sa
ba ka jin magana ta ne, Ko na yi k**ar na yi
banza? Na ce ka bar mugun wasa da yarinyar
nan, sai ka ki. Haka bara ka dauke ta ka je
yawon ku na banza na farauta; ka sa yarinyar
mutane ta yi ta muggan mafarkai. Yanzu kuma
shi ne ka ce ku yi tsere za ka je da ita farauta?
To wallahi in na ji ko da wasa ka dauki Inno
zuwa kowane irin yawo ne – ba ma na farauta
ba – sai mun yi hannun riga ni da kai!”
Adamu ya shige dakin sa, da alamar bai ji
dadin fadan nan da Umma ta yi ma sa ba; Inno
ta san Adamu ba ya son Umma na yi ma sa
fada, sai ta ji da ta sani da ba ta yi gudu sosai
ba har ta fadi ta ji ciwo. Umma ta zauna ta na
ta mumula ma ta goshin har ya rage girma
sa’annan ta sa aka kira mai cire targade ya cire
ma ta. Aka shafa ma ta magani a kafar da kuma
goshin ta.
Tun daga wannan lokaci har ta koma Gulubba
ba ta kara ganin Adamu ba. Sai bayan mako
biyu ya je Gulubba ya je ya gaishe da Umma ya
tarar ta tafi wajen biki a ’Yartsakuwa. Ita kuma
Inno ta je gidan kakar ta a Unguwar Fulani. Sai
matan Yayyen ta kawai ya samu. Inno ta dawo
ke nan ta yi kicibis da shi a kofar gida ya na
shirin hawa keken sa. Bayan ta gaishe shi ya ce,
“Me ki ka je yi wajen wannan tsohuwar
guzumar?”
“Kai Yaya! Gwaggon ce tsohuwar guzuma
kuma? Ni dai ba ruwa na in su Umma s**a ji ka
na ce ma uwar su tsohuwar Guzuma.”
“Ke dai kin cika tsoro Wallah! To ko ba
tsohuwar ba ce, su ma sun san tsohuwa ce.
Yanzu dai ki zo gobe, gab da magariba mu
hadu a fadama, za mu je farauta. Amma fa kar
ki gaya ma kowa?”
Cikin kagara Inno ta ce, “To. Na gode Yaya sai
na zo.”
Kar ka so ka ji yadda zuciyar ta ta cika da
murna. Har ta kosa safiyar ta waye. Ta san dai
idan Umma ta sani sai ta kusa kashe ta da
duka.
Wanshekare kuwa Inno ta ce za ta je Tumfafi ta
kwana. Da ma koyaushe ta tambaya ta je can
ana barin ta. Tun da la’asar ta bar gida, amma
dai ta yi ta tsaye-tsaye a hanya har sai da ta ga
magriba ta gabato sosai, sannan ta saki hanya
ta ruga da gudu sai fadamar nan. Ta na isa ta
tarar da Adamu. Ya k**a hannun ta su ka ruga
da gudu kallon faduwar rana. Bayan ta fadi su
ka yi alwalla su ka yi salla, sa’annan Adamu ya
fara shirin zuwa yawon farauta. Ya sanya fitilar
mafarauta ta gaban goshi, ita ma ya ba ta wata
ta sanya. Ya dauko bindigar sa ya duba ta
sosai, ya sagala a kafada ya dauki kwari da
bakan sa ya rike a hannu, sa’annan ya mika wa
Inno tocilar hannu ta rike. Daga nan ya gargade
ta da in za ta yi magana ta rinka yi a hankali
kuma ta rinka tafiya sannu-sannu, amma ba da
sando ba. Kafar sa takalmi ne na leda wanda
yake boye karar takun tafiya. Ita ma ya fito da
wani wanda ya yi mata ya ba ta ta sanya,
sa’annan ya yi gaba, ta na bin sa a baya, su ka
dinga kutsawa cikin dutsen. Tun dai su na bi ta
inda Inno ta san ta taba zuwa har su ka shiga
daji sosai, inda ta fara jin koke-koken namun
jeji. Yau Adamu bai zo da karnukan sa ba. Su
ka shiga wani daji, ta ga birai ma su yawa
wadanda sai ihu su ke yi don sun gan su. Su ka
shiga wani dajin kuma amma shiru ya ke k**ar
da dai duniya ba mahalukin da ya taba shiga
cikin sa, amma sai ta ga Adamu ya tsaya ya na
ta kalle-kalle. Ya rada ma ta a hankali in ta ga
wani dabba a wajen ta nuna ma sa. Ita ma ta
rinka kura ido sosai yadda ta ga Adamu na yi.
Can a bayan wata bishiya sai ta hango wani abu
na kyalli. Da ta haska da fitila sai ta ga ashe
idon wata dabba ce wacce ba ta taba ganin irin
ta ba. Mamaki ya cika ta, ta ce ‘Lah! Yaya ji
ba!” Ta ko yi maganar ne da karfi wanda ya
firgita wannan dabbar, ta fincika da gudu. Ko
da juyowar da Adamu ya yi har ta yi nisa.
“Haba Fati! Ba na ce ki rinka magana a hankula
ba? Kin ga ga shi kin sa ta gudu.”
“Yi hakuri Yaya. Na manta ne. Yaya, ya sunan
waccan dabbar?”
“Sunan ta gada,” inji shi.
“Yaya, da yanzu harbe ta za ka yi?”
“A’a. So na ke in dauke ta in kai ta can wani
waje in boye, in ba haka ba in wasu maharban
sun zo kashe ta za su yi. Da akwai su da yawa a
cikin dutsen nan, amma yanzu saura ’yan
kadan; duk an kashe su, sauran ba su fi goma
ba. Shi ya sa nake son in sake musu waje inda
ba wanda ya sani kafin a karasa da su duka.”
“Yaya, wai da akwai zaki a dutsen nan?”
“Da har giwa ma akwai, manoma su ka
karkashe su saboda su na ma su barna a
gonakin su. Kuma da akwai kura, jakin dawa da
sauran su, amma duk ’yan farauta sun karasa
da su.”
Daga nan su ka ci gaba da tafiya a hankali su na
duddubawa. Zuwa can Inno ta ji wani abu
k**ar nishi a gefen hagun ta. Da ta haska sai ta
ga wata dabba ce a kwance. Ta je a hankali ta
kira Adamu ta nuna ma sa. Da ya duba sai ya
ga ashe wata gada ce ta haihu, ’ya’ya uku,
amma haihuwar ta jigatar da ita, don haka har
ma ta mutu, amma da alama ba ta dade da
mutuwa ba. Da ya duba jariran sai ya ga biyu
sun mutu amma daya da sauran ran sa. Adamu
ya dauke shi, shi ma sai numfashi ya ke yi da
kyar, ya kusa mutuwa. Ya bude goran sa na
ruwa ya dan zuba ma sa a kai, sa’annan ya zuba
masa a cikin bakinsa. Jaririn gadar ya yi
gwauron numfashi, sannan ya sake yin lakwaf.
Adamu ya sake jirkita shi, ya matsa wajen uwar
ya k**a kan nonon ta guda ya saka ma sa a
baki, ya dinga matso ruwan nonon zuwa cikin
bakin dan a hankali har ya farfado ya dan bude
idon sa, sa’annan ya sake rufewa. Inno kuwa
murna ta cika zuciyar ta, ganin Yaya Adamu ya
ceci wannan dan marayan gadan, ga shi har ya
fara farfadowa. Zuwa can ya fara tsotsar nonon
da kan sa. A hankali dai har ya sha ya koshi,
sa’annan ya saki nonon ya na kallon su. Ya kura
musu ido. Zuwa can ya k**a wutsi-wutsi, ya na
wani irin kuka. Adamu ya aje shi a hankali ya
taka da kafar sa, ya fadi, ya sake tashi ya yi taku
daya ya sake bingirewa. Da ya sake tashi Inno
ta ce a hankali, “Yanzu zai mike Yaya.” Shi kuwa
Adamu ya kalle ta ya yi murmushi. Sai ga shi
kuwa dan dabbar nan ya na mikewa ya yi tafiya
bai fadi ba, ya je ya na ta sunsunar ’yan’uwansa
da uwarsa.
Adamu ya mike ya ce da Inno ta tashi su koma
gida. Sa’annan ya dauki dan jaririn gadar.
“Yaya, a nan za mu bar sauran?”
“E. To ina za mu da su?”
“Kai Yaya! Don Allah mu je da su mana a yi
masu kabari?”
“A’a, Inno. Bari gobe na dawo inin rufe su.
Yanzu kin ga dare ya yi.”
Su ka juya su ka koma inda su ka fito har cikin
dajin dutsen zuwa sarari inda mutane su ke.
Kafin su karasa ne s**a ga wani dabba inda
Adamu ya yi sauri ya auna sa kibiya, ya kuwa yi
sa’a ya same shi. Adamu ya zo ya dauke shi.
Ashe neme sun isa inda ’yar bukkar Adamu ta
ke ke nan aka tsuge da ruwa. Da ma ya yi ’yar
bukka saboda irin wannan lokacin; ya gina ta ne
da kananan mulmulallun dutsuna, sa’annan ya
bi ya like su da sumunti, ya yi ’yar kofa ta itace.
Ya yi sauri ya bude ma su su ka shige ciki.
Bayan k**ar minti goma aka dauke ruwan. Su
ka fito waje, iska mai dadi ta na ta kadawa.
Inno ta hau kan wani dan karamin mulmulen
dutse. Adamu ya isa wurin ta, ya lura ta na
kallon taurari ne, ga farin wata kuma ya haske
ko’ina. Samaniya ta yi gwanin kyau k**ar ta
tsaya haka har abada. Ruwa kuma ya wanke
dutsen, itace sun yi shar gwanin ban sha’awa,
sai kadawa su ke yi a hankali. Dutsen ya yi wani
irin kyau na musamman. Iska sai kanshin ruwan
sama ta ke yi.
Inno ta yi wani gwauron numfashi na farin ciki,
ta juya ta kalli Adamu. Shi kuwa ya yi ma ta
murmushi. Sai ta ji ina ma a ce duniyar ta tsaya
haka a daidai wannan lokacin har abada.
“Bari in je in soya ma na naman can. Ko ba ki
jin yunwa ne?” Adamu ya tambaye ta.
Sai dai kawai ta girgiza kai domin a lokacin nan
zuciyar ta ta kar ta ke. Ba abin da ya dame ta a
duniya.
Adamu ya hura wuta a falalen dutsen, ya
babbaka naman bayan ya yayyanka shi. Ya
gyara shi ya zuba a tukunya tare da albasa,
daddawa da gishiri da dan ruwa kadan. Ya
dora a kan wuta. Kan ka ce kwabo wurin ya
game da kanshi mai tsinka yawu. Da man
naman reme akwai shi da mai. Bayan ya soyu.
Adamu ya shimfida musu tabarma su ka zauna
su na ci suna hira. Bayan sun gama su ka sha
ruwa, sa’annan su ka shiga hira. Ya na ba ta
labaran farauta, ya fara yi ma ta wa
tatsunniyoyi barci ya kwashe ta. Shi ma Adamu
ya yi shimfida ya kwanta.
Can da dare ya yi zurfi Inno ta farka ta ga
Adamu ya na salla. Ita ma kawai sai ta yi
alwalla ta rinka bin sa. Lokacin da s**a gama
nafilfilin, har asuba ta yi. Su ka yi salla asuba
tare da raka’atanil fajr. Inno ta dama musu
fura su ka karya. Su ka k**a hawan wani
kololon dutse har sai da su ka kai can saman
tsinin sa, sannan su ka zauna su na fuskantar
gabas inda alfijir a lokacin ya fito ya yi haske.
Daga bayan su kuma ga wata da taurari ba su
karasa shigewa ba.
Duk zagaye da su duhu ne, sai jaja-jajan hasken
alfijir wanda a hankali ya fara bajewa sa’annan
hasken safiya ya fara haska wajen. Saman ta yi
shudiya sosai, ba hadari ko girgije ko daya. Su
na nan zaune sun yi shiru, rana ta fara kunno
kai daga can nesa a hankali k**ar mai jin
kunya. Su ka kalli juna su na yi murmushi. Ba
wanda ya yi magana domin babu bukatar yin
ta. Su kadai su ka san abin da su ke ji a wannan
lokaci. Ga Iko da Iyawa ta Ubangiji su na gani a
gaban su. Can Adamu ya bude baki, ya nisa, ya
ce, “Lallai! Godiya duka ta tabbata ga Allah
madaukakin Sarki. Allah mun gode ma ka da
rahamomin da ka rahamta mu da su.”
Su na nan zaune har rana ta karasa fitowa,
haske ya bazu ko’ina. Inno ta ce, “Yaya Adamu,
don Allah yi ma ni busa ma na.” Ita dai ta na
son ta ji Adamu ya na busa sarewar sa.
Adamu ya fito da sarewar sa ya fara busawa a
hankali busa mai dadi da sa farin cikin rai da
narkar da zuciya. Inno ta rufe ido. Duk sai ta ji
wani dadi ya lullube ta. Ta tsunduma cikin wani
kogi na tunani da soyayya. Ita kam a duk
duniya in ka debe iyayen ta to ba wanda ya kai
Yaya Adamu. Komai ta ce ta na so a duniyar
nan ya na yi ma ta sai dai in ba shi da ikon sa.
Su na nan a haka har gari ya waye sosai. Su ka
tashi su ka k**a hanyar gida. Adamu ya raka ta
bakin gari sa’annan ya koma gida. Ita dai Inno
ta san har karshen rayuwarta ba za ta mantawa
da wannan lokacin ba.