26/07/2026
*HON. DR. ABUBAKAR KABIR BICHI YA RANTSAR DA SABBIN MA’AITAKAN LAFIYA NA WUCIN GADI DON KARFAFA HARKAR LAFIYA A BICHI*
Babban Bikin Rantsar da Sabbin Ma’aikatan Lafiya na Wucin Gadi da Hon. Dr. Abubakar Kabir Abubakar Bichi, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazabar Bichi da kuma Shugaban Kwamitin Kula da Kasafin Kudi na Majalisar ya dauki nauyi, na gudana a jiya 25 ga watan yuli 2026 a babban filin wasa na makarantar firamaren hagagawa.
Aikin ya samo asali ne daga damuwar Hon. Bichi na ganin an inganta harkar lafiya a cikin mazabarsa, tare da rage matsin da asibitoci da cibiyoyin lafiya ke fuskanta na rashin isassun ma’aikata.
Da yake jawabi a wurin taron, Hon. Bichi ya bayyana cewa daukar ma’aikatan na wucin gadi mataki ne na gaggawa domin tabbatar da cewa mazauna Bichi sun samu kulawar lafiya mai inganci, musamman a lokacin da gwamnati ke kan aikin daukar ma’aikata na dindin.
Ya ce: _"Lafiya ita ce tushen ci gaba. Ba za mu iya magana kan ilimi ko noma ba idan jama’ar mu ba su da lafiya. Saboda haka na ga ya zama wajibi mu tallafa wa asibitocin mu da karin hannu domin yin aiki yadda ya kamata."_
Manufar Shirin:
1. Cike Gibin Ma’aikata: Sabbin ma’aikatan za su tallafawa manyan asibitoci da PHCs a fadin Bichi LGA wajen baiwa marasa lafiya kulawa cikin gaggawa.
2. Damar Samun Aikin Yi Wa Matasa: Wannan shiri ya ba da damar aikin yi ga matasa masu digiri da difloma a fannin lafiya daga mazabar Bichi.
3. Inganta Hidimar Lafiya: Ana sa ran shirin zai rage yawan marasa lafiya da ke jiran dogon lokaci, tare da inganta tsafta da kulawa a wuraren lafiya.
Ma’aikatan da aka dauka sun hada da Nurses, CHEWs, Lab Technicians, da sauran kwarru a fannin lafiya. Kowannensu zai tura shi wata cibiyar lafiya daban-daban a cikin karamar hukumar.
Shugabannin asibitoci, limaman gari, sarakunan gargajiya, da al’ummar mazabar Bichi sun yaba wa Hon. Bichi bisa wannan jajircewa, inda s**a ce wannan na daga cikin ayyukan da s**a fi tasiri kai tsaye ga rayuwar talaka.
Taron ya samu halartar manyan baki ciki har da Wakilan Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Dan majalissar jaha mai wakiltar karamar hukumar bichi, shugaban karamar hukuma, Shugabannin Jam’iyya, da Iyayen Daukacin ma'aikatan da aka dauka.
Hon. Member ya sanarda shirinsa na daukaka darajar asibitin bichi inda zai dawo karkashin kulawar Asibitin koyarwa na Malam aminu kano, da daga darajar asibitocin saye da danzabuwa zuwa Asibitin bai daya dake karkashin kulawar gwamnatin jaha (general hospital) domin rage cinkoso a babban asibitin bichi,
Allah ya sakawa member da alkhairi ya jikan magabata ya karawa hajiya lafiya, Allah yayi riko da hannayensa yayi masa kakakin majalissa ta 11,
Bello Abdullahi Bichi.
25, yuli, 2026.
Matashiyya Multi Media Bichi
HON. DR. ABUBAKAR KABIR BICHI COMMISSIONS TEMPORARY HEALTH WORKERS TO BOOST HEALTHCARE IN BICHI
Babban Bikin Rantsar da Sabbin Ma’aikatan Lafiya na Wucin Gadi da Hon. Dr. Abubakar Kabir Abubakar Bichi, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazabar Bichi da kuma Shugaban Kwamitin Kula da Kasafin Kudi na Majalisar ya dauki nauyi, na gudana a yau 25 ga watan yuli 2026 a babban filin wasa na makarantar firamaren hagagawa.
Aikin ya samo asali ne daga damuwar Hon. Bichi na ganin an inganta harkar lafiya a cikin mazabarsa, tare da rage matsin da asibitoci da cibiyoyin lafiya ke fuskanta na rashin isassun ma’aikata.
Da yake jawabi a wurin taron, Hon. Bichi ya bayyana cewa daukar ma’aikatan na wucin gadi mataki ne na gaggawa domin tabbatar da cewa mazauna Bichi sun samu kulawar lafiya mai inganci, musamman a lokacin da gwamnati ke kan aikin daukar ma’aikata na dindin.
Ya ce: _"Lafiya ita ce tushen ci gaba. Ba za mu iya magana kan ilimi ko noma ba idan jama’ar mu ba su da lafiya. Saboda haka na ga ya zama wajibi mu tallafa wa asibitocin mu da karin hannu domin yin aiki yadda ya kamata."_
Manufar Shirin:
1. Cike Gibin Ma’aikata: Sabbin ma’aikatan za su tallafawa manyan asibitoci da PHCs a fadin Bichi LGA wajen baiwa marasa lafiya kulawa cikin gaggawa.
2. Damar Samun Aikin Yi Wa Matasa: Wannan shiri ya ba da damar aikin yi ga matasa masu digiri da difloma a fannin lafiya daga mazabar Bichi.
3. Inganta Hidimar Lafiya: Ana sa ran shirin zai rage yawan marasa lafiya da ke jiran dogon lokaci, tare da inganta tsafta da kulawa a wuraren lafiya.
Ma’aikatan da aka dauka sun hada da Nurses, CHEWs, Lab Technicians, da sauran kwarru a fannin lafiya. Kowannensu zai tura shi wata cibiyar lafiya daban-daban a cikin karamar hukumar.
Shugabannin asibitoci, limaman gari, sarakunan gargajiya, da al’ummar mazabar Bichi sun yaba wa Hon. Bichi bisa wannan jajircewa, inda s**a ce wannan na daga cikin ayyukan da s**a fi tasiri kai tsaye ga rayuwar talaka.
Taron ya samu halartar manyan baki ciki har da Wakilan Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Dan majalissar jaha mai wakiltar karamar hukumar bichi, shugaban karamar hukuma, Shugabannin Jam’iyya, da Iyayen Daukacin ma'aikatan da aka dauka.
Hon. Member ya sanarda shirinsa na daukaka darajar asibitin bichi inda zai dawo karkashin kulawar Asibitin koyarwa na Malam aminu kano, da daga darajar asibitocin saye da danzabuwa zuwa Asibitin bai daya dake karkashin kulawar gwamnatin jaha (general hospital) domin rage cinkoso a babban asibitin bichi,
Allah ya sakawa member da alkhairi ya jikan magabata ya karawa hajiya lafiya, Allah yayi riko da hannayensa yayi masa kakakin majalissa ta 11,
Bello Abdullahi Bichi.
26, yuli, 2026.
Matashiyya Multi-Media Bichi