31/07/2025
Wasu daga cikin abokan Imam Hasan ɗan Ali (a.s) sun rubuta masa wasiƙar ta’aziyya saboda rasuwar ’yarsa. Sai ya rubuta musu:
"Bayan haka: Na samu wasikarku da kuke ta’aziyya a kan rasuwar ’yata wadda ta rasu. Na danganta lamarinta ga Allah cikin biyayya da hukuncinSa da haƙuri a kan jarabarsa. Lallai masifu suna cutar da mu, bala’o’i suna gigita mu game da masoyan da muka saba da su, waɗanda s**a kasance suna nuna kulawa da mu, da abokai masu kauna waɗanda idon mai kallo yana farin ciki da ganinsu kuma idanunmu suna samun kwanciyar hankali da su. Amma kwanakin duniya sun sare su, mutuwa ta riskar da su, har s**a bar bayin da za su gada kuma mutuwa ta shafe su. Suna cikin jerin mamata, suna makwabtaka a wuri guda, amma ba irin makwabtaka ta rayuwa ba—babu hulɗa ko ziyara ko saduwa duk da kasancewa kusa. Jikinsu suna nesa da iyalansu, babu mai kula da su, an bar su da kuma barin mallakansu. Danginsu sun rabu da su, babu wanda ke kula da su yanzu. Ban ga gida kamar gidansu ba, ko matsuguni kamar nasu ba; a cikin gidaje masu ban tsoro da wuraren kwana masu firgi. Sun koma waɗancan wuraren masu ban tsoro, s**a fita daga gidajen da suke morewa, s**a rabu da su ba don ƙiyayya ba, sun bar su ga lalacewa. Ita yarinyar da ta rasu, baiwa ce da nake da ita, ta bi hanyar da kowa ke bi daga farko zuwa ƙarshe—na farko sun riga sun bi wannan hanya, na baya ma za su biyo bayanta. Sallama a gare ku."
Daga Imam Hasan (a.s): "Lalle Allah yana da birane biyu, guda a gabas ɗaya a yamma, kowace tana da shingaye na ƙarfe da ƙofofi miliyan daya na zinariya. A kowanne, mutane na magana da harsuna kibkib—saba’in miliyan, kowanne da yare daban. Ni na san dukkan yarukan, kuma ban da ni da Hussaini (kanina) babu wani hujja a cikinsu."
Hasan (a.s) da Abdullahi bn Abbas sun kasance a kan tebur. Sai wani tsutsa ya sauka a teburin. Abdullahi bn Abbas ya tambaye shi: "Me ke rubuce a fikafikan tsutsar?" Sai Imam Hasan (a.s) ya ce: "
Duba ƙarashen a comment section.
Honer Mikiya