Los Blancos Hausa

Los Blancos Hausa 🤩🎉 Los Blancos Hausa – shafi ne da ke kawo muku sabbin labarai, rahotanni, da dukkan abubuwan da s**a shafi Real Madrid cikin harshen Hausa. 🔵⚪

🚨 YANZU-YANZU: Florentino Pérez ya riga ya fara aiki a ɓoye domin ɗauko ɗan wasan Michael Olise.Ana tattaunawa kai tsaye...
06/06/2026

🚨 YANZU-YANZU: Florentino Pérez ya riga ya fara aiki a ɓoye domin ɗauko ɗan wasan Michael Olise.

Ana tattaunawa kai tsaye da mutanen da ke da hannu a yarjejeniyar domin ganin an kammala cinikin.

Los Blancos Hausa

🚨 LABARI Da DUMI-DUMI: Bayern Munich ba su da niyyar amincewa da tayin Euro miliyan 150 da Real Madrid ta yi kan Michael...
05/06/2026

🚨 LABARI Da DUMI-DUMI: Bayern Munich ba su da niyyar amincewa da tayin Euro miliyan 150 da Real Madrid ta yi kan Michael Olise.

Ko da Real Madrid ta ƙara tayin zuwa Euro miliyan 200, Bayern za ta ƙi, domin ta kuduri aniyar ci gaba da riƙe shi a kulob ɗin.

Sai dai hukuncin ƙarshe zai dogara ne da abin da ɗan wasan da kansa yake so.

Los Blancos Hausa

🚨🚨 Florentino Pérez ya sanar da cewa Real Madrid za ta tura tayin da ya kai €150 miliyan, wanda zai zama sabon tarihi a ...
04/06/2026

🚨🚨 Florentino Pérez ya sanar da cewa Real Madrid za ta tura tayin da ya kai €150 miliyan, wanda zai zama sabon tarihi a kulob ɗin

“Zai kasance tayin hukuma na €150m ga wani fitaccen ɗan wasa na duniya! Zan aika da tayin ranar Talata,” in ji Florentino Pérez.

Wane ɗan wasa ne wannan?

Los Blancos Hausa

🚨 DA DUMI-DUMINSA: Florentino Pérez ya yi imanin cewa João Neves ne ɓangaren da ya rage domin cika ƙarfin tsakiyar fili ...
04/06/2026

🚨 DA DUMI-DUMINSA: Florentino Pérez ya yi imanin cewa João Neves ne ɓangaren da ya rage domin cika ƙarfin tsakiyar fili na Real Madrid.

Ana kuma cewa João Neves shi ne ɗan wasan da Florentino Pérez ya fi so a cikin zaɓuɓɓukan da ake dubawa.

Majiyar labari: Alberto Pereiro.

Los Blancos Hausa

🚨 DA DUMI-DUMINSA: Real Madrid na neman ɗan bayan da zai iya taka leda a matsayin tsakiyar baya (centre-back) da kuma ha...
04/06/2026

🚨 DA DUMI-DUMINSA: Real Madrid na neman ɗan bayan da zai iya taka leda a matsayin tsakiyar baya (centre-back) da kuma hagu na baya (left-back).

Ƙungiyar ta riga ta fara tuntuɓar wakilan Riccardo Calafiori.

Haka kuma, Joško Gvardiol na cikin 'yan wasan da ƙungiyar ke matuƙar sha'awa, amma ana ganin samun sa zai kasance da wahala.

Los Blancos Hausa

🚨 A HUKUMANCE: An zaɓi ƙwallon da Arda Güler ya ci a ragar Elche CF a matsayin Mafi Kyawun Ƙwallo na Kakar La Liga.🏆 Wan...
04/06/2026

🚨 A HUKUMANCE: An zaɓi ƙwallon da Arda Güler ya ci a ragar Elche CF a matsayin Mafi Kyawun Ƙwallo na Kakar La Liga.

🏆 Wannan ƙwallon ce aka ayyana a matsayin Goal of the Season a gasar La Liga.

Los Blancos Hausa

🚨 DA ZAFI ZAFINSA 🚨✅: IBRAHIMA KONATÉ YA ZAMA SABON ƊAN WASAN REAL MADRID A HUKUMANCE! 🤍💣An kammala yarjejeniya kan kwan...
04/06/2026

🚨 DA ZAFI ZAFINSA 🚨✅: IBRAHIMA KONATÉ YA ZAMA SABON ƊAN WASAN REAL MADRID A HUKUMANCE! 🤍💣

An kammala yarjejeniya kan kwantiragin shekara huɗu wanda zai ɗaure shi da Real Madrid har zuwa watan Yunin 2030.

Konaté zai koma Real Madrid bayan zaɓukan ƙungiyar, inda zai zama ɗaukar ɗan wasa na farko da Florentino Pérez ya yi. 🤝🏿

𝐃𝐔𝐌𝐅𝐑𝐈𝐄𝐒 ➕ 𝐊𝐎𝐍𝐀𝐓𝐄 ➡️ AN KAMMALA KOMAI A HUKUMANCE! 🤍🔥

Los Blancos Hausa

🚨💣 LABARI NA MUSAMMAN!Denzel Dumfries ya kammala gwajin lafiyarsa (medical) domin komawa Real Madrid. 🔐Real Madrid ta ai...
03/06/2026

🚨💣 LABARI NA MUSAMMAN!

Denzel Dumfries ya kammala gwajin lafiyarsa (medical) domin komawa Real Madrid. 🔐

Real Madrid ta aika wa Inter takardun hukuma domin kunna sharadin siyan sa na €20m a yau, kuma Dumfries ya yi gwajin lafiyarsa a Holland.

✅ HERE WE GO, AN TABBATAR DA KOMAI KASHI 100% 🇳🇱⚪

Magoya bayan Real Madrid, yaya kuke ganin wannan sayen? 👇🔥

Los Blancos Hausa

🚨🔥 Yanzu-Yanzu: Enrique Riquelme ya bayyana cewa:🗣️ "Babban ɗan wasan da zan sanar da shi a daren yau na iya zama Erling...
03/06/2026

🚨🔥 Yanzu-Yanzu: Enrique Riquelme ya bayyana cewa:

🗣️ "Babban ɗan wasan da zan sanar da shi a daren yau na iya zama Erling Haaland*. Haka kuma yana iya zama wani babban tauraron ƙwallo na duniya."* 🌟💣

Los Blancos Hausa

Barcelona ta biya Euro miliyan 80 domin wai yazo yana dribbling wannan, kai anya wannan tsarin mai yiyuwa che kuwa? 😭Da ...
03/06/2026

Barcelona ta biya Euro miliyan 80 domin wai yazo yana dribbling wannan, kai anya wannan tsarin mai yiyuwa che kuwa? 😭

Da ni ne Gordon, da tuni na tafi kai tsaye zuwa Saudiyya.

Wannan saƙon yana bayyana ra'ayi ne ko barkwanci na mai rubutawa, ba hasashen gaskiya ko labarin hukuma ba ne

Los Blancos Hausa

Address

Bauchi
740102

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Los Blancos Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category