29/08/2026
🚨🔵🔴 ATLETICO MADRID BA TA DA IKON HANA SHI — KO FIFA MA! 🤯
Julián Álvarez na iya samun wata hanya ta tilasta komawarsa Barcelona kafin a rufe kasuwar musayar ƴan wasa, duk da cewa Atlético Madrid ta sha nanata cewa ba za ta taɓa tattaunawa da Barça a kansa ba. 😳
A cewar rahoton GiveMeSport, wata tsohuwar dokar Spain mai suna Royal Decree No. 1006 na ba ƙwararren ɗan wasa damar kawo ƙarshen kwantiraginsa da kansa. Idan hakan ta faru, batun diyya zai koma gaban kotu domin a tantance adadin kuɗin da Atlético za ta samu.
Rahoton ya kuma ce FIFA ba za ta iya shiga tsakani ba, saboda wannan lamari ya shafi ƙungiyoyi biyu daga ƙasa ɗaya, kuma batun zai kasance ƙarƙashin tsarin shari'ar Spain.
Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne, rahoton ya ce Barcelona na iya ɗaukar nauyin biyan wannan diyya. Adadin ba lallai ya kai ga €490M na release clause ɗin Julián ba, domin kotunan Spain na iya kallon irin waɗannan manyan release clauses a matsayin masu tsauri.
⏳ Barcelona har yanzu na son cimma yarjejeniya da Atlético kafin 1 ga Satumba, amma idan Atlético ta ci gaba da ƙin tattaunawa, Julián na iya ɗaukar mataki da kansa domin ganin burinsa na komawa Barcelona ya tabbata. 🔵🔴👀
Shin Julián ya kamata ya yi amfani da wannan dokar ya koma Barcelona? 🤯🔵🔴
[GiveMeSport / Mundo Deportivo / GOAL]